Gwamnan Bauchi Ya Karya Farashin Kayan Noma Za a Saida Buhun Taki Kan Dubu 20

Gwamnan Bauchi Ya Karya Farashin Kayan Noma Za a Saida Buhun Taki Kan Dubu 20
 

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kaddamar da shirin noma na 2024 domin taimakawa manoma da takin zamani a farashi mai rahusa. 

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sayarwa manoman Bauchi takin zamani na NPK kan kowane buhu a kan N20,000 kuma za a rage tsadar kayan noma. 
A wurin kaddamar da shirin a garin Dass, Bala Mohammed ya ce gwamnatin Bauchi ta ware N300m domin inganta harkokin noma. 
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter. 
Gwamna Mohammed ya ce sabon shirin zai maida hankali wajen bullo da hanyoyin bunƙasa noma kuma zai samar da sinadarai da kayan noma na N50m. Ya kuma yabawa ACRESAL, shirin noman da ya fi shahara a Bauchi, inda ya jaddada kudirinsa na aiwatar da ingantaccen tsarin noman zamani a faɗin jihar.