Shugabancin APC a Neja: Garba Dukku ne yafi cancanta
Shugabancin APC a Neja: Garba Dukku ne yafi cancanta
A daidai lokacin da jam'iyyar APC ke kokarin kafa turakun shugabancin jam'iyyar daga matakin gundumomi zuwa jiha da kasa baki daya, wanda a jihar Neja tayi nisa wajen sulhunta 'yan takarkaru da ya bata nasarar kammala zaben shugabanni a matakin zuwa gundumomi, zuwa yanzu wasu kananan hukumomin jihar sun yi nisa wajen kammala sulhu tsakanin 'yan takarkarun shugabancin jam'iyyar a matakin kananan hukumomi kafin ranar biyu ga watan satumba mai kamawa da za a tabbatar da shugabancin kananan hukumomi.
Kafin nan dai uwar jam'iyyar a matakin jiha bisa shirinta na canja mukaman yankuna uku na jihar ta mayar da shugabancin jam'iyyar zuwa yankin Neja ta arewa ( Zone C), inda yanzu haka karamar hukumar Bargu tana da dan takara guda daya, yayin da karamar hukumar Kontagora ta ke da yan takarkaru guda uku, sai karamar hukumar Wushishi mai dan takara daya, yayin da karamar hukumar Rijau tsohon dan takarar kujerar majalisar wakilai kuma tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar, Alhaji Garba Muhammed Dukku shi ma ya nuna sha'awarsa na yin takarar kujerar shugabancin jam'iyyar bisa dalilan dawo da martabar jam'iyyar da samun shugabancin jam'iyyar na kwarai kamar yadda ya bayyana a lokacin hira da manema labarai.
Dukku ya cigaba da cewar jam'iyyar APC ba ta da matsala a wajen jama'a domin sun gamsu da irin rawar da take takawa wajen ayyukan cigaban kasa hakan ne yasa duk da takon sakar da akai ta samu a baya tsakanin gwamnati da shugabannin jam'iyyar bai dadata da kasa ba, yace idan yayan jam'iyyar suka ba shi dama zai tabbatar ya dunke duk wata kusurwa da ta huje wajen hada kan yayan jam'iyyar da gwamnati dan baiwa kowa damar taka rawa a siyasance.
Dukku yace jam'iyyar APC a Neja bata da matsala da yayanta kuma ba ta da matsala da gwamnati illa rashin fahimtar da ta taso tsakanin gwamnati da shugabannin jam'iyyar da suka gabata, zan tabbatar na baiwa kowani dan jam'iyya damar da ta dace bisa tsarin dokokin jam'iyya wajen janyo dukkan masu korafi a jiki dan basu damar sanin halin yadda jam'iyya ke tafiyar da harkokin yau da kullun da kuma baiwa gwamnati shawarwarin da suka dace wajen kawo cigaban kasa da goyon baya ta yadda jam'iyyar za ta samu damar cigaba da kafa tubalan da suka dace na cigaban kasa kamar yadda ake bukata.
Abdulmajeed Mas'ud ( Fashion B) jigo ne a jam'iyyar kuma na hannun damar gwamnati a karamar hukumar Rijau, ya bayyana cewar matakin da uwar jam'iyya ta dauka a matakin jiha abin a yaba ne. Domin hakan zai warkar da kurjin da ya dade yana zafi a zukatan al'umma, baiwa jama'a damar yin sulhu dan kaucewa rarrabuwan kawuna zai taimakawa jam'iyyar wajen fitar da nagartattun yan takara a babban zaben kasa mai zuwa na 2023.
Fashion B, yace yanzu muna da yan takarkarun shugabancin jam'iyyar a matakin jiha, amma duba da irin kudurorin Alhaji Garba Muhammed Dukku shi yafi cancanta yayan jam'iyya su mara wa, saboda ana bukatar nagartattun shugabannin jam'iyya da suke da kwarewa kuma suka san matsalolin jam'iyya da zasu iya magance su a kankanin lokaci.
Tsohon dan siyasa ne da yayi takarar kujerar majalisar wakilai kuma ya taba neman kujerar gwamnan jiha, yana da dubarun janyo kowa a jika ta yadda za a samar da gwamnatin da za ta samu goyon bayan jama'a ta yadda gwamnati za ta samu nasarori akan abubuwan da ta sanya a gaba, kamar yadda na fahimci akidun Garba Dukku mutum ne mai gaskiya da ke tsayuwa akan abinda zai taimaki kasa da al'umma.
Ina da tabbacin jam'iyyar APC za ta cigaba da jan ragamar mulkin jihar nan saboda irin turbar da gwamnati mai ci ta Alhaji Abubakar Sani Bello ta assasa wanda jama'a ba zasu ga alfanun hakan ba a yanzu, domin jihar nan an mata rutse da yawa dole kuma warkawa sai an bi a hankali.
managarciya