Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Abdulaziz Yari----Sanatan Bauchi

Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Abdulaziz Yari----Sanatan Bauchi


Tsohon mataimakin masu rinjaye a majalisar dattawa ta bakwai, Abdul Ningi ya ce akalla sanatoci 67 ne ke mara wa Abdulaziz Yari baya a neman takarar shugabancin majalisar.

 Ningi ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da ‘yan jaridu, ya ce lokaci ya yi da za a bari ‘yan majalisa su zabi shugabanninsu. 
Yari wanda yake wakiltar Zamfara ta Yamma kuma tsohon gwamnan jihar ya na daga cikin wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar majalisar. 
“Lissafinmu na baya-bayan nan, ya nuna cewa a jiya Talata 6 ga watan Mayu, mambobi na kara nuna goyon bayansu. 
“Ni ba dan jam’iayyar APC ba ne, ban san yadda kwamitin tsare-tsarensu ya ke ba, amma shekaru 20 kenan ana samun matsala saboda kakaba wa ‘yan majalisa shugabanni tun lokacin Enwerem da Chuba.
“Ya kamata a bari mambobi su zabi wandanda suke so a ra’ayi na, jam’iyyar PDP sun yi kuskure makamancin wannan, ya kamata APC su guji aikata haka, kamar yadda jam’iyyar ta zabi shugabanta haka ya kamata majalisar ma su zabi shugabanninsu.