Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni ya tserewa tsara

Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni ya tserewa tsara

Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni Honarabul Ayuba Dantudu yana aiki tuƙuru don kawo cigaba a ƙaramar hukumarsa sama da kowane shugaba daga cikin ƙananan hukumomi 23 na jihar Sakkwato.
A bincike da kafar yada labarai ta MANAGARCIYA ta gudanar ya nuna shugaban ba abin da ya sanya a gaba sai aiki, matsalar tsaron da ake fama da shi bai hana shi kurɗawa a dukkan lungu da saƙo na ƙaramar hukumar, a ɗan ƙanƙanen lokacin da yake jagorancin jama'a.
Honarabul Ayuba ya gyara rukunin gidajen Alu a ƙaramar hukumar wanda ya laƙume kuɗade da dama, an kammala aikin a ƙanƙanen lokaci wanda ake gani da ba jajirtaccen mutum ne ya shiga gaba a aikin ba, za a kwashe shekara ana yinsa.
Ayuba Dantudu ya mayar da hankali sosai a fannin tsaro in da yake ta faɗi tashi a tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro don ganin muradin al'ummarsa ya cika a wannan gwamnati ta Dakta Ahmad Aliyu Sokoto da ikon Allah yankin Sabon Birni zai zauna lafiya.
A yanzu Honarabul na aiki kan kiyon lafiya, inganta noma, dawo da martabar ilmi da samar da aikin yi ga matasa kusan ko'ina ya taba a haujin inganta rayuwa.