Buhari Ya Amince Da Sharadina Kafin Mu Fara Tafiyar Siyasa----Bola Tinubu

Buhari Ya Amince Da Sharadina Kafin Mu Fara Tafiyar Siyasa----Bola Tinubu

FASSARAR MAGANGANUN DA JAGABAN YA SAKI DA HARSHEN YARBANCI CIKIN BACIN RAI….

 
“Idan ba don ni dake nan tsaye a gabanku ba, da ace na yi taurin kai, na buga ganguma na yaki, na shedawa Buhari cewa mu daura damarar fada kuma na yi tsayin dakan cewa ba zan hada kai da shiba, da bai zama shugaban kasa ba.
 
“Ya yi takara karo na daya da na biyu da na uku, ya sha kaye, kuma har ga talabijin ya shiga yana kuka bayan yayi rantsuwa ba zai kara tsayawa takara ba, amma na je na same shi a Kaduna nace masa ya daina kuka saboda wannan ba lamari ne na kuka ba kuma zan goya masa baya kuma nayi masa alkawalin samun nasara.
 
“Abu daya kuma dana fada masa shine kada ya yi abinda ba dai-dai ba ga kasar Yarbawa, kuma ya amince.
 
“Tun da ya hau karagar mulki ban taba rike mukamin minista ba, ban yi baran gari da miya ba, ko kuma in roke shi samun wata kwangila ba, ban kuma roke shi fura ba, ko kuma na dauki bashi.
 
“Abin da kawai nake cewa shine lokaci ne, da ya kamata masu magana da harshen Yarbanci su zama shugaban kasa kuma cikin kabilar Yarabawa, lokaci na ne.
 
“Na dauki yaran siyasa da yawa kuma na basu kariya, amma idan ana fuskantar hadari, mutum ya fara kare kansa.
 
“Nayi hidima sosai. Ba na son in zama tarihi. Lokaci na ne na zama shugaban kasa. Al'amari ne na hakki a gare ni.
 
"Wannan abin da na kare 'ya'yana na siyasa ya isa, ba na son su mayar da ni tarihi kawai," in ji Tinubu yayin ziyarar tuntuba da ya kai jihar Ogun, a ranar Alhamis, 2 ga Yuni, 2022.