Bai dace a cire tallafin Man Fetur ba, Kwankwaso ya fadi abin da yakamata a yi

Bai dace a cire tallafin Man Fetur ba, Kwankwaso ya fadi abin da yakamata a yi

 

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake magana kan cire tallafin man fetur. Kwankwaso ya ce a cikin maidu'in da suka fitar na ayyukan alheri da za su yiwa Najeriya a bayyane yake. 

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X. 
Kwankwaso ya ce ba tallafin mai ba ne ya kamata a fara tabawa ba akwai wasu abubuwa da dole sai an dakile su. 
Jigon NNPP ya ce dole gwamnati ce kadai za ta dakile almundahana da ta'asa da ake yi game da tallafin mai. 
"Ku je ku duba maidu'inmu kan maganar cire tallafin mai, mu a cikin littafinmu yana nan." 
"Kuma na tabbata in ba dukanku ba to tabbas wasunku suna da shi a tare da su" 
"Abin da muka ce shi ne ka da ka taba tallafi, ka tafi inda ake badakala da ta'asa ka dakile." 
Kwankwaso ya ce babu wanda zai iya dakile karairayi da ake yi kan tallafin mai sai gwamnati. 
Ya ce ana kawo jirgin ruwa biyu zuwa uku amma sai a rubuta a ce guda daya ne duk wannnan gwamnati ce za ta iya maganinsu.