A Ɓangaren Ayyukan Raya Ƙasa Ne Sanata Barau Ya Ciri Tuta----Muryar Arewa

A Ɓangaren Ayyukan Raya Ƙasa Ne Sanata Barau Ya Ciri Tuta----Muryar Arewa

Daga Habu Rabeel Gombe

Gamayyar kungiyoyin al'ummar Kano ta arewa Voice of the North Kano, sun yabawa Sanatan su Barau Jibrin wajen gudanar da ayyukan ci gaba da raya al'umma.

Kungiyar kuma tayi Allah wadai da wasu batagarin matasa Yan ta'adda da suka yi batanci a harabar zauren Majalisar Dattawa ta kasa.

Shugabannin gamayyar kungiyar ta Muryar Kano ta arewa Voice of Kano North sun yi Kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da Shugabannin majalisun tarayya da Ma'aikatar shari'a ta kasa da cewa su yi watsi da kiraye- kirayen da wasu batagarin ke yi akan a cire Sanata Barau daga shugabancin Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dattawa, Inda suka ce yin hakan katsalandan ne wa Majalisa.

Kungiyoyin sun nuna takaicin su game da  yadda aka dauko wasu tsirarun  mutane wadanda ba yan yankin Kano ta Arewa ba domin yin zanga-zangar nuna batancin ga wakilin na su.

"mutanen arewacin Kano, sune suka dace suyi kira akan a cire  wakilin su, wanda al'umma suka shaida irin ayyukan da yake aiwatarwa a  yankin nasu ba sojojin haya ba". Inji Voice of Kano North.

Da yake Zantawa da manema labarai mai magana da yawun kungiyar Ambassada Iman Kabir Umar, " yace duk Najeriya babu Sanatan da ya yiwa mazabar sa aiki Kamar Sanata Barau Jibin.

Ambasada Iman Kabir, yace lokaci ba zai isa a iya bayyana ayyukan da Sanatan ya gudanar ba amma ya zayyana wasu kadan daga cikin su da suka hada da gina jami'ar Karatu daga gida ta (National Open University) a kananan Hukumomi goma Sha 13, da yake wakilta.

Ya Gina matsakaitan filayen wassanni (Mini stadium)  a kananan Hukumomi 13, ya Gyara manyan Asibitoci na kananan Hukumomin da yake wakilta, ya raba motoci da babura da Kwamfutoci ga Daliban Kano ta Arewa, ya Gina kwalejin 'Yan sanda a Karamar Hukumar Kabo ya Gyara manyan titunan da suke yankin Kano ta Arewa.

Kungiyar tace Barau, ya Sanya fitulu masu aiki da hasken lantarki a Kananan Hukumomi 13 da yake wakilta, ya raba motoci ga dalibai, sarakuna, da Yan Hisba da kungiyoyin addini, ya Gyara Azuzuwan karatu da Kuma Gina sababbi a kananan Hukumomi 13 da yake wakilta.

Sannan ya rabawa manoma jari don inganta harkar noma a kananan Hukumomi 13 da yake wakilta, wadanan kadan ne daga cikin Ayyukan da Sanatan ya gudanar a yankin sa 

Daga nan sai Ambasada Iman ya godewa Sanatan tare da alkawarin ci gaba da mara masa baya don ganin ya sauke nauyin da yake kansa.