PDP Tafi APC Sau Dubu---Tambuwal

PDP Tafi APC Sau Dubu---Tambuwal

 

Darakta janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya ce jam’iyyarsa ta fi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sau dubu. 

Jaridar Punch ta rahoto cewa Tambuwal, wanda shine gwamnan jihar Sokoto ya yi bayanin dalilin da yasa PDP ce jam’iyyar da tafi dacewa da zama zabin yan Najeriya a babban zaben 2023 mai zuwa. 
Gwamnan ya bayyana cewa yayin da PDP ta nuna adalci a tikitinta na takarar shugaban kasa, sam tikitin APC bai nuna dabi’ar tarayya ta Najeriya ba.
Tambuwal ya bayyana cewa APC ta haifar da sabani a kasar, yana mai cewa PDP za ta yi aiki don tabbatar da ganin cewa irin haka bai sake faruwa ba. 
Gwamnan na jihar Sokoto ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kamfen din jam’iyyar a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. 
Sai dai kuma, ya bayyana cewa PDP tana da tikitin Atiku/Okowa wanda ya tabo kowani bangare na Najeriya.