Maganar komawar Kwankwaso APC ta fara ɗaukar sabon salo
Jita-jitar cewa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da jagoransa Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa APC ta fara ɗaukar sabon salo, duk da rashin tabbataccen bayani daga bangarorin biyu.
Masu lura da al’amuran siyasa na cewa idan wannan ya faru, zai iya canza alkiblar siyasar Kano gaba ɗaya kafin zaben 2027.
A watan Satumba ne Kwankwaso ya fara tayar da kura, lokacin da ya bayyana cewa zai iya komawa APC amma bisa “manyan sharudda”.
Ya ce a baya an yi masa siyasar danniya daga wasu jiga-jigan APC, don haka dole sai an bayyana abin da NNPP za ta amfana kafin komawa.
A cewarsa: “Muna shirye mu koma APC amma ba za mu yarda a yi amfani da mu a jefar da mu gefe ba. Sai an faɗa mana abin da NNPP za ta samu.”
Wannan magana ta haifar da damuwa a cikin APC, musamman ga masu shirin neman takarar gwamnan Kano a 2027, domin komawar Kwankwaso na iya rushe musu lissafi.
Sai dai har yanzu babu tabbaci daga bangaren Kwankwaso ko Gwamna Abba, duk da cewa rahotanni na nuna ana tattaunawa a bayan fage tsakanin manyan ‘yan siyasar.
A yanzu haka, Kano ta shiga wani sabon yanayi na rikitarwar siyasa, inda kowanne bangare ke sa ido kan ko Madugu da Abba za su yanke shawarar da ka iya girgiza dandalin siyasa a jihar.
managarciya