WATA UNGUWA: Fita Ta 38

WATA UNGUWA: Fita Ta 38

BABI NA TALATIN DA TAKWAS

 

Ficewar shi ke da wuya Irfan ya miƙe yana safa da marwa a tsakiyar ofishin kai ka ce aikin hajji yake. Wutar damuwar da ke cin zuciyarsa ta daɗa ruruwa.

'Ya ilahi! Yanzu matar da zan aura ce ta zama taxi motar kowa? Anya kuwa zan yarda da wannan?'

Sai kuma ya shiga girgiza kai, 'Ina kai! Ba zai yiwu ba abotar kura da akuya, Maheerah 'yar malamai ce da ta ƙoshi da tarbiyya ba za ta taɓa saka kanta a halaka tana ji tana gani ba.'

Wata zuciyar ta tunatar da shi, yayin da wani sashi na zuciyarsa ya faɗa masa cewar "Ka manta da laifin da ta aikata har Abbanta ya kore ta daga gida ne? Idan kuma ɓacin rai ya yi silar ƙulluwar baƙin zare a zuciyarta fa? Mai yiwuwa ta zaɓi wannan hanyar ne don ɗaukar fansa.'

Kamar wanda aka laftawa makeken ice a gadon baya haka ya zabura ya kwashi maƙullan motarsa daga kan teburinsa ya fice da hanzari kamar zai wuce ƙafarsa. Idanunsa sun kaɗa sun yi jazir tamkar waɗanda aka zubawa jar kala a ciki.

Tun bai ƙarasa inda motarsa take a fake ba, ya danna madannin hannunsa a take motar ta yi ƙara alamar ta buɗe, da sassarfa ya isa ciki ya yi mata key tare da barin farfajiyar ma'aikatar tasu.

 

Ma'eesh da fitowarsa kenan daga motarsa zai shiga ciki don ganawa da Irfan a kan al'amarin Maheerah, sai kawai ya hango faɗawarsa mota da hanzari ya fisge ta. Hakan ce ta saka Ma'eesh ɗin ya tsaya a wuri ɗaya cak yana bin motar Irfan da kallo.

A ɗan bayyane ya ce "To fa! Wannan kuma saurin me yake yi haka?"

 

Ganin ba zai samu amsa ba ya saka shi ciro waya daga aljihunsa ya dannawa Irfan kira, sai dai har ta ƙaraci ɓurarinta bai daga ba. A haka sai da ya jera masa kira uku amma bai ɗaga ko ɗaya ba.

Ganin hakan ya saka shi mayar da wayar a aljihun wandon jamfar da ke jikinsa ya ɗaga kafaɗa sama yana faɗar "Kai ka jiyo, a yi mutum sai zafin ran tsiya?"

Ya juya zuwa motarsa a ransa yana faɗar 'Yanzu haka wani ne ya sanar da shi abin da na zo faɗa masa a kan wannan fingalalliyar yarinyar shi ne yake fushi. Da ma a kanta bai da haƙuri ko kaɗan.'

 

Daga haka ya ja motarsa shi ma ya bar ma'aikatar, bai yi ƙoƙarin bin bayan Irfan ba ya ɗauki hanyar da za ta sada shi da inda ya kudurci zuwa a ransa.

 

**

 

Irfan kuwa bayan ficewarsa bai zame ko'ina ba sai gidansu, bai yi yunƙurin shiga sashen iyayen nasa ba kamar yadda ya saba zuwa gaida su a kowacce rana bayan dawowarsa daga aiki. Duk da ya tabbatar Abbansa yana gida a lokacin. Don kuwa ganin motar Abban kaɗai ya isa alamta masa hakan.

 

A dame ya yi cikin ɗakin, sai ya zauna akan kujera sai kuma ya miƙe ya hau gado, ya sake miƙewa.

 

Kusan mintuna goma ya kwashe a hakan kafin zuciyarsa ta ɗarsa masa wani abin da ya saka shi yin zumbur, ya ɗauko wani zungureren littafi take kan bedside drawer ya ciro biro daga aljihunsa sai da ya gama rubutun, ya ɗaga takardar da kyau ya sake bibiyarta don ya tabbatar saƙon ya fita da kyau.

Can ya naɗe ta yana furzar da Iska sannan ya ajiye ta a cikin jakar aikinsa ya faɗa banɗaki don yin wanka.

 

Bayan ya fito kuma shi ne ya kwanta don ya samarwa ƙwaƙwalwarsa biyu, amma sai hakan ya gagara.

 

A ranar dai haka ya wuni a birkice, fuskarsa ta birkice zuwa wani irin yanayi da baka isa ka gane damuwa ce ko firgici ba.

 

Washe gari tun wuraren ƙarfe takwas na safe ya tashi daga bacci ya shirya ya shiga sashen iyayensa don gaida su tare da yin break fast kamar yadda suka saba.

Bayan sun gaisa da Hajiya ya ɗale dinning yana faɗar "Hajiya don Allah zuba mini abincin nan sauri nake."

Ta kalle shi da murmushi "Haba kai kuwa Irfan, ka manta da al'adar gidan nan ne? To bari na tuna maka al'adar gidan nan ce cin abinci tare ka jira fitowar Alhaji da Idris mana sai mu ci tare."

Fuska ba yabo ba fallasa ya ce "Hajiya sauri nake za ni gun aiki, yau ɗaya a mini afuwa zan saɓa al'adar gidan."

Bata sake ce masa komai ba ta zuba masa abincin ya fara ci a hankali kamar mai tauna magani. A zahiri gangar jikinsa kawai ce a wurin amma ruhinsa yana birnin Balgori. Tuni ruhinsa da ƙwaƙwalwarsa suka fara shawagi a birnin a cikin duniyar mafarkinsa. Shi ya sa ba shi da burin da ya wuce zuwa can a yanzu.

 

Yana Fatar ya samu yadda yake so a wurin aiki. A gaggauce ya gama cin abincin ya miƙe, a dai-dai lokacin ne kuma Alhajinsa ya shigo falon ganin shi ya sanya Irfan ya shimfiɗa yanayin walwala a fuskarsa ya matsa kusa da alhajin tare da rissinawa ya gaishe shi.

 

Alhajin ya Dube shi cikin Murmushi "Masha Allah! Har ka shirya zuwa aikin kenan?"

Irfan ya gyaɗa kai Alhajin ya ce "Allah shi yi albarka."

Ya amsa da amin, har ya buɗi baki zai ce wani abu kuma sai ya fasa ya miƙe ya juya zai tafi.

Alhaji ya ce "Na ga bakinka na motsi da alama akwai Magana a laɓɓanka, me kake son faɗa ne?"

 

Ya amsa masa da bakomai shi zai tafi. Iyayen nasa suka raka shi da addu'ar fatan dacewa da nasara a cikin dukkanin al'amuransa. Sannan ya fice daga falon.

 

A zahirin gaskiya yana so ne ya faɗa wa alhajin nasa cewar shi zai ɗauki dogon Hutu a wurin aiki zai je neman matarsa abar ƙaunarsa. Har ya so ya nuna masa takardar shigar da buƙatarsa da ya rubuta zuwa ga hukumar gudanarwar ma'aikatar tasu. Amma sai ya fasa. Bakomai ne ya saka shi yin hakan ba sai don tunawa da ya yi cewar mahaifin nasa zai iya dakatar da shi daga wannan yunƙurin musamman idan ya ji dalilin neman hutun. Ya gwammace ya ci gaba da ɓoye musu wannan sirrin har zuwa lokacin da zai samo Mahee ya dawo da ita mahaifarta.

 

****

 

A can birnin Balgori kuwa tun ranar da Maisha ta sanar da Mahee luv zancen zuwan Jafsee birnin, ta fara shirye-shiryen tarbarsa. Sai dai shirin da take yi ba na maraba ba ne da masoyi shiri ne irin na ɗaukar fansa. Tarba ce ta wulaƙancin da son cika nufi akan wanda take harin. Don haka ta kirawo Maisha da London girl suka haɗu a gidanta suna ƙara kitsa zaruruwan makircin da ba su gama haɗawa ba.

 

London girl ta kalli zumbulelen hijabin da ke hannun Mahee ta kalli Maisha cike da shaƙiyanci ta ce "Tab! Maisha ki ce gobe zaki sha zafi, duk da tsanar da kika yi masa. Wannan uban hijabin sai ka ce matar Liman?"

Maisha ta murmusa kana ta ce "Kin manta ni yar limamin unguwarmu ce a yadda na faɗa masa? Idan ban saka wannan ba wace shiga zan yi ya yarda da ni?"

Suka yi dariya dukkan su, Mahee ta ce "Ni ai ba ma Maisha ce abin dariya ba oga Bash nake son gani cikin shigar limamai." Suka tuntsire da dariya a haka suka kwashe sa'o'i masu yawa kafin kowaccen su ta fita sabgar gabanta.

 

Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta yi kunya, a wata ranar Asabar da misalin ƙarfe 7am na safe Jafsee da iyayensa suka kama hanyar birnin Balgori kowannensu cikin shiga ta mutunci. Ja'afar har da hula dara a kansa ya sha malum-malum. Abin da tun tashinsa ya yi wayo ba zai iya tuna ranar da ya yi amfani da ita ba.

 

Bayan shafe doguwar tazara mai tsayin gaske motar sufurin gwamnatin da suke ciki ta faka a tsakiyar babbar tashar birnin.

 

Cike da farin ciki Ja'afar ya sauko daga motar yana bin ko'ina na tashar da kallo, farinciki yake ji sosai a cikin zuciyarsa. A ransa ya ce 'Allah sarki! Yau ni ne a mahaifar matata, ban taɓa zaton cewa zan yi aure da wuri haka ba sai a dalilin shigowar Mardee a rayuwata. Tabbas waya ta zamo silar alkhairi a gare ni, ga shi zan auri yar mutunci ba kamar sauran watsatsin yanmatan da na yi a baya ba.' ya faɗa a ransa.

Da alama ya manta cewar Ubangiji ba ya goyon bayan zalunci kuma duk abin da ka shuka shi zaka girba idan khairan, khairan idan kuma sharran sharan ɗin ce dai zaka girba.

 

A lokacin da direba yake ƙoƙarin kunce kayan matafiyan da ke bayan mota, Ja'afar ya koma gefe yana neman layin Maisha, sai dai har kira uku a jere bata ɗaga ko ɗaya ba, bayan kafin ma su taso sai da ya sanar da ita haka ko a mota ya yi magana da ita awa uku baya. Ai Yakamata ace ta ajiye wayar a kusa da ita.

 

Sai kawai ya sake danna mata kira cikin yanayin mamaki a nan mamakinsa ya ƙaro domin a wannan karon ma wayar aka she take, haka ya yi ta gwada wa har sau uku a kashe.

 

Nan fa ya ji mummunar faɗuwar gaba ta ziyarce shi 'To me ya faru, me hakan ke nufi? Yanzu ya zai yi kenan?'

Waɗannan tambayoyin ne suka ziyarci zuciyarsa kafin ya tuna bai san kowa ba a garin ga kuma iyayensa da yake tare da su.

 

A dai-dai lokacin ne Babansa ya matso kusa da shi yana faɗar "Jafaru yaya, ka samu yarinyar ne?"

 

Cikin sanyin jiki ya ce "Da fari layin ya shiga, yanzu kuma na ji a kashe."

 

"To ka kira wani daga cikin ahalinta mana, babanta ko yayanta haka." Ɗayan abokin tafiyar na su ya faɗa.

Ja'afar ya ce "Ban da ita wallahi bansan number kowa a daginta ba, hasali ma ko gaisawa ban taɓa yi da su ba ko a waya."

 

Suka zazzaro idanu waje babansa ya ce "Amma shi ne ka kwaso mu zuwa nan garin da baka ma da tabbacin yarinyar a nan take ko ƙarya ta yi maka?"

 

"A yi hakuri Abba, bari dai na siya mana abinci mu ci kafin ta yi chaji, ina kyautata zaton batırın wayar ne ya yi ƙasa, nasan tana can tana fafutukar neman chaji."

 

Da wannan ya lallaɓa su ya siya masu abinci a tashar suka zauna suna ci da ma ba su ɗauko wani kaya ba.

 

A ɓangaren Maisha kuwa da ma sun riga sun ƙirga awannin tafiyar don haka suka kwatankwaci dai-dai lokacin, tana ganin kiransa ta tabbatar sun ƙaraso ne, shi ne London girl ta bada shawarar a ɗan ja shi a ƙasa ya fara ɗanɗana kuɗar shi kafin ya zo ya tarad da abin da yafi wancan. Shi ne dalilin da ya saka Maisha ta kashe wayar sai kwasar dariya suke yayin da Mahee da ke zaune a gefe tana tunano cin fuskar da ya yi mata take tunanin 'Anya ɗan wannan hukuncin kawai ya wadatar ya fahimtar da shi girman kuskurensa?'

 

 

UMMU INTEESAR CE