Ƴan bindiga sun sace shugabannin APC biyar a Zamfara
Ƴan bindiga sun sace manyan jiga-jigan jam’iyyar APC guda biyar a jihar Zamfara.
TheCable ta rawaito daga shafin Zagazola Makama, cewa ƴan jam’iyyar APCn duk ‘yan asalin karamar hukumar Kaura Namoda ne, kuma an sace su ne a jiya Asabar yayin da su ke tafiya zuwa yankin Marafa na jihar.
Rahotannin sun ce ‘yan siyasar da aka sace suna hanyarsu ta zuwa gidan Sanata Abdulaziz Yari, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, lokacin da ‘yan bindiga suka tare su suka yi garkuwa da su.
Daga cikin wadanda aka sace akwai Yahaya Sani Dogon Kade, shugaban mazabar Dan Isah, da kuma Bello Dealer, shugaban mazabar Sakajiki.
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, don tabbatar da aukuwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
managarciya