Labarin Ciwon Labarin Ciwon HERNIA Da Yanda Za'a Magance Shi
Ciwon kaba, wani ciwo ne da ke faruwa saboda gajiyawa ko raunin jikin naman da ya rufe ciki (wato naman da yake
karkashin fatar da ta taso tun daga kahon zuci har zuwa mara), wadda kan sa tsagewar wani bangare na naman. Hakan ke sa halittun jikin dan Adam na ciki, kamar hanji ya fito ta wannan
’yar kafa.
ABUBUWAN DAKAN KAWO (KABA)
Abubuwan da ke kawo ciwon kan ka su kashi biyu kamar haka:
1. Gado (Congenital): Ana gadon ciwon tun a ciki, sai jariri ya fito da ita kabar.
2. Wanda ake samu daga baya (Acquired): Wannan nau’i ne da ake kamuwa bayan an girma saboda raunin naman jiki, sanadiyar KIBA sosai ko kuma tsananin aikin da zai wahalar da jiki kamar daukar abu mai nauyi. Duk lokacin da wani bangare na naman jikin mutun ya samu gajiyawa sakamakon daukar nauyi, ko tari na tsawon lokaci, ko ma tsananin yunkuri lokacin ba haya, duk sukan sa naman ya rabu biyu, ta yadda wani sashe na ’ya’yan hanji zai biyo hanyar.
Shan taba sigari ma kan sa mutun ya kamu da cutar saboda tsananin tari sanadiyyar ciwon huhu da sigari ke sa wa.
IRE-IREN SA
Iren-iren ciwon: Ciwon ya fi yawa ne a mahadar kashin cinya da kugu (Inguinal and Femoral Hernia), gefen al’aura.
1- Akwai wadda ke faruwa a saman layin da ya raba kirji zuwa cibiya gida biyu (Epigastric Hernia). Wannan nau’in ya fi shafuwar maza a kan mata. Sama da kashi 75 na cutar a maza aka fi samun ta.
2-Sai wadda ke faruwa a cibiya, takan faru ne idan aka samu gajiyawar jijiyoyin jini da ke kawo jini ga cibiyar. Wannan nau’in kan auku ga yara sa’annan takan bayyana sosai a shekarun 3 zuwa 4 ko ta zauna har tsawon rayuwa idan ba a dau mataki ba.
Iyaye kan lura da ciwon a lokacin da yaro ya yi tari, za ta fito a gefen cibiya.
3-Sai wadda ke faruwa sanadiyyar daukar ciki ko haihuwa ga mata a mahadar kashin cinya (Femoral Hernia).
4-Akwai kuma wadda ke faruwa sanadiyyar fida (Surgical Hernia). Wannan tana faruwa ne sanadiyyar matsalolin da ba a rasa ba, wani lokacin idan aka yi fida, musamman idan babu
kyakkyawar kulawa a gefen da aka yi fidar.
ALAMOMIN KABA
Alamomin cutar:
1- Mutun zai rika jin wani abu ya fada masa a wani bangaren jiki ko ya fice.
2- Sai kuma jin zafi, kamar kuna a bangaren da abun ya faru.
3- Sai kumburi ko a ji dan kululu.
4- Jin zafi lokacin daukar wani abu mai nauyi, ko yayin tari. Zafin kan bazu zuwa sauran bangarorin jiki kamar baya, kafa
ko al’aura.
HANYAR MAGANCE CIWON
Hanyar magance ciwon: Hanya mafi inganci domin kawar da ciwon kaba shi ne fida, domin a gyara wannan wuri da yake rauni. Idan kuma aka ki zuwa a yi aikin, to ciwon ba ya mutuwa da kansa sai dai ya kara girma wani lokaci kuma ya rika zafi sosai, wanda hakan barazana ce ga rayuwar mutum.
Bayan aikin fida mutun zai ji rashin walwala da dan zafi na ’yan kwanaki, kafin ya fara jin sauki. Hakan kan dauki sati daya zuwa shida kafin a ji garau. Amma wadanda ke daukar nauyi ko aiki mai wahala, to za su dauki tsawon lokaci kafin su warke.
Allah yakara mana lafiya, marasa lafiya Allah ya Basu lafiya.
Lafiya Uwar Jiki
l
Da Yanda Za'a Magance Shi

managarciya