APC Ta Rasa Jigo A Sakkwato

APC Ta Rasa Jigo A Sakkwato

Ɗaya daga cikin jigogin jam'iyar APC a jihar Sakkwato kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sakkwato ta Arewa  Honarabul Abdullahi Hassan ya fita daga jam'iyar APC.
Abdullahi Hassan a takardar da ya aikawa Managarciya a Talata bai bayyana jam'iyar da zai koma ba a nan gaba sai dai ya nuna ya fice daga APC daga ranar Talata 14 ga watan Juli 2022.

Takardar da aikawa shugaban mazaɓarsa ta Magajin gari "B" ya ce ya yanke hukuncin ne domin cigaban ƙaramar hukumarsa da jiha da ƙasa baki ɗaya.

A jihar ta Sakkwato masu sharhin siyasa na ganin da wuya ba PDP zai koma ba duk da bai bayyana ba.