Ku Zabe Ni Za Ku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki A Kyauta-----Tinubu 

Ku Zabe Ni Za Ku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki A Kyauta-----Tinubu 

Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya ce zai magance matsalar biyan kudin wuta idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023. 

Tinubu yayi wannan maganar ne a wajen kaddamar da wani kasuwanci wanda yan kasuwa suka samar mai suna Bussines Forward, jiya Talata a Lagos.
"Ta Kowacce Hanya sai kun samu wuta, a kyauta ba tare da biya kudin wuta ba, idan na zama shugaban kasa, duk wani batu na wuta zai wuce, ku rubuta ku ajiye" 
Tinubun yayi alkawarin maida Nigeria wata cibiyar habaka kasuwanci, yana mai cewa zai cire tallafin man fetur saboda Nigeria ba za ta ci gaba da baiwa wata kasa arzikinta ba.
"Ya zamu rinka ba da tallafin mai ga kasar Camerron ko Niger Ko Benin, duk halin da aka shiga kamata yayi ace mun cire tallafin fetir sai muyi amfani da shi wajen bunkasa fannin ilimin mu." 
Tsohon gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta bawa bangarori wanda bana gwamnati ba dama, za su sakar musu mara wajen gudanar da aiyukansu. 
Jaridar NairaLand ta rawaito cewa tinubu yayi alakawarin samar da wutar lantarki awa ashirin da hudu tsawon kwana bakwai muddin aka zabe shi. 
Tinubun na fadin hakan ne ta hannun mai taimaka masa kan kafafen sadarwa.
Tinubu yace idan aka zabe shi zai hada hannu da 'yan kasuwa wajen da kungiyoyi ko bangarorin da ba na gwamnati ba wajen bunkasa harkokin kasuwanci, da habaka samar da abubuwan da 'yan Nigeria ke bukata.