SDP ba ta shiga hadaka ko yarjejeniya da kowace jami'ya a Sakkwato--Sakatare

SDP ba ta shiga hadaka ko yarjejeniya da kowace jami'ya a Sakkwato--Sakatare
 
 
Jami'iyar SDP a matakin jihar Sakkwato ta nisanta kanta kan wani taro da tsohon dan takarar gwamna a jam'iyar Sanata Abubakar Umar Gada ya yi na  tara wasu  mutane a sanya alamar jam'iyyar a matsayin an yi hadaka da ADC.
 
Bayanin na kunshe a cikin takardar da aka rabawa manema labarai da sakataren jam'iya a Sakkwato Dahiru Umar Aliyu ya sanyawa hannu bayan kammala taro da shugabannin jam'iya a jiha a ofishinsu dake birnin jiha.
 
Ya ce SDP a matakin kasa sun haramta yin amfani da kowace alama ko sunan jam'iya ba tare da izinin shugabannin kasa ba, yin haka da aka yi a Sakkwato na tara taro da sunan SDP na iya kawo daukar mtakin Shari'a.
 
"Alluna da hotuna da aka yi amfani da su a wurin taron da ke dauke da alamar SDP ya sabawa dokar jam'iya."
 
Bayanin ya soki Sanata Gada da ya tara taron, ya ce tun bayan da aka kammala zaben 2023 dan takarar gwamnan bai sake kula magoya bayan SDP a matakin jiha sai dai kawai a ganshi a wasu taruka na daban.
 
"Majalisar zartarwa ta jiha na kara tabbatarwa jama'a ba su shiga kowace hadaka ba  ko yin magana da wata jami'ya ba, kan haka ba ruwanmu da kowace hulda da wani zai yi da wata jami'ya," kalaman Sakatare.
 
A satin da ya gabata ne tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya zo Sakkwato in da ya gana da wasu magoya bayan SDP da nufin sun amince za su shiga jam'iyar ADC a yi hadaka da su, hakan ya sa SDP a matakin jiha ta nisanta kan ta da su duk da dan takarar gwamnan Sakkwato Sanata Abubakar Umar Gada da ya yi wa jam'iyyar takara a zaben da ya gabata na cikin mahalarta da suka shirya zaman.
 
Wakilinmu ya tuntubi Sanata Gada kan lamarin ya ce wadanda ke maganar ba ma 'yan jam'iyar SDP ba ne, ba wanda ya sansu a jam'iyar, shugaban jam'iaya a matakin jiha ya san da tafiyarsu kuma komai a bisa doka da ka'ida suke yinsa.