Babu inda aka yi amfani da kuɗin Legas a yaƙin neman zaɓena na 2023 - Atiku
EFCC na bincike kan zargin an yi amfani da kuɗin Legas wajen daukar nauyin yaƙin neman zaɓen Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa ya karɓi kuɗi daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ta hannun Aisha Achimugu domin yaƙin neman zaɓensa na 2023.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe ya fitar ranar Alhamis, 27 ga watan Maris ta bayyana rahotannin a matsayin wata "gagarumar ƙarya".
Sanarwar ta bayyana rahotannin a matsayin wani yunƙuri na ɓatawa Atiku suna domin faɗaɗa manufofin siyasar shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Sanarwar ta cigaba da cewa Atiku Abubakar bai san gwamna Sanwo Olu ba, kuma bai taɓa ganinsa ba, balle ya tura masa waɗannan kuɗi.
EFCC dai na binciken Aisha Achimugu ne wadda ke da kusanci da gwamnan na Legas kan badaƙalar wasu kuɗi da ake zargin ta tallafawa yaƙin neman zaɓen Atiku da su a 2023.
Ana ganin dangantaka ta fara sukurkurcewa tsakanin gwamnan na Legas da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ake ganin shi ya haddasa wannan binciken.
Jaridar Daily Trust ta yi ƙoƙarin jin ta bakin fadar shugaban ƙasa da EFCC kan wannan batu, amma haƙarta bata cimma ruwa ba.
managarciya