Wamakko ya fadi dalilinsa kan kin sukar Tambuwal

Wamakko ya fadi dalilinsa kan kin sukar Tambuwal
 

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya fadi dalilinsa kan kin sukar tsohon gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a gidajen reidiyo.

 
Sanata Wamakko ya ce baya zagin shugabanni don sun bar mulki wanda ya bar mulkin Sakkwato bayan ya kammala wa'adinsa na  shekara 8, "Aminu Tambuwal kanena ne ni na kawo shi bana sukarsa a kafafen yada labarai ba shi ne ra'ayin siyasa ta ba.
An tambaye shi ko siyasar ubangida nada hadari ya ce, "Akwai siyasar ubangida dake da hadari wadda ake yi a wasu wurare wadda ba sha'awar jama'a ce ake kulawa ba, amma in da ake fifita ra'ayin jama'a."