Jarman Sakkwato Ya Bar Jam'iyar PDP Zuwa APC

Jarman Sakkwato Ya Bar Jam'iyar PDP Zuwa APC

 

Jarman Sakkwato Alhaji Ummaru Kwabo A.A ya bar jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC in da zai cigaba da gudanar da siyasarsa.

Jarman Sakkwato a wani jawabi da Abdulkadir Dan'iya ya yi a gaban dimbin magoya bayansu a gaban Jarma ya ce a 2023 jam'iyar APC za a yi daga sama har kasa.
Dan'iya ya ce a takarar shugaban kasa za a zabi Bola Tinubu, a matakin Gwamna kuma za a zabi Gwamna waton Amadu Dan Jarma da Alu.
Wannan bayanin ne ke nuna cewa sun sauya sheka kan abubuwan da suke ganin ba a yi masu adalci ba a kan tafiyar PDP a matakin jiha da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta.
Abin da Sakkwatawa ke jira a cikin wannan canjin shekar ita ce matsayar da mataimakin gwamna Manir Dan'iya zai dauka bayan ya dawo daga aikin Umara da ya tafi.
Sakkwatawa sun san wannan rashin fahimtar da aka samu ta taso ne tun bayan da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bai aminta da mataimakinsa ya gade shi ba a 2023.
Matsayar Manir Dan'iya abar jira ce ga mutanen Sakkwato domin ba kasafai ake ganin an shiga kishi da fadan mutum ba ya kuma barka da dubararka, kan haka ake ganin duk irin  hukuncin da su Jarma suka dauka shi ne na Manir Dan'iya, saboda kishin abin da aka yi masa ne silar yafe tafiyar PDP a zukatansu.