PDP Ce Za Ta Samu Nasara A Zaben 2023-----Tambuwal

PDP Ce Za Ta Samu Nasara A Zaben 2023-----Tambuwal

h2>PDP Ce Za Ta Samu Nasara A Zaben 2023-----Tambuwal

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa jam'iyar PDP ce za ta samu nasara a zaben 2023 dake tafe domin sun shirya tsaf su karbi ragamar mulkin Nijeriya a hannun APC.

Gwamnan ya furta haka a ranar Assabar a wurin babban taron jam'iyyar a filin taron na Eagle dake Abuja.

Ya ce ina farincikin sanar da cewa wadanda suka raba mu su raunata mu sun sha kasa mu ne muka yi nasara jam'iyarmu ta karfafa cikin hadin kai.

Tambuwal ya zayyano wasu nasarori da PDP ta samarwa kasar Nijeriya a shekara 16 da ta yi na mulkin kasa.