Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Hannu a Harin Ayarinsa 

Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Hannu a Harin Ayarinsa 

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya sha alwashin zakulo duk masu hannu a harin da aka kaiwa ayarinsa ranar Lahadi domin doka ta yi aiki a kansu. 

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda wasu 'yan daba suka yi ruwan duwatsu kan Ayarin gwamnan yayin da suke hanyar komawa daga wurin kamfe.
Punch ta ce Lamarin dai ya faru ne sa'ilin da gwamna da yan tawagarsa ke hanyar komawa daga wurin gangamin kamfen PDP da aka gudanar a kananan hukumomin Silame da Wamakko. 
Daga cikin manyan mutanen dake Ayarin har da 'yan takarar gwamna a Sakkwato da Kebbi karkashin inuwar PDP, Mallam Saidu Umar da Janar Aminu Bade da sauyan manyan jiga-jigan siyasa. 
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da masu rike da mukaman siyasa, Tambuwal yace tuni aka yi ram da wasu daga cikin maharan. 
"Abun takaici ne muna hanyar dawowa daga Wamakko ranar Lahadi, a daidai ofishin Aliyu Magatakardan Wamakko, wasu 'yan daba suka farmaki Ayarina zamu gidan gwamnati." "Ba zamu lamurci kowace kalar iskancin rikici ba a jihar Sakkwato, ba zamu yarda a yi wasa da zaman lafiyarmu ba. 
Ina kira da manyan siyasa su guji ta da yamutsi, su umarci magoya bayansu da yin kamfe mai tsafta."