Siyasar Sakkwato ce ta mamaye batun tsige sarkin musulmi

Siyasar Sakkwato ce ta mamaye batun tsige sarkin musulmi

Batun za a tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya fara ne tun a siyasar 2019 a lokacin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal yake neman sake zama Gwamnan Sakkwato a karo na biyu, in da abokan hamayar Tambuwal suka zargi Sarkin da mara masa baya ya kyale su.

A haka aka yi shiga zaben na 2019 ana zargin akwai tsamin dangantaka tsakanin magoya bayan APC da  sarki har ‘yan adawa  suka rika rera waken ‘sabon Gwamna, sabon Sarki’.

Bayan da aka dawo zaben 2023 tsamin dangantakar ya rage sosai domin jagororin adawa a lokacin sun kai ziyarar girma da neman addu’a a fadar Sarkin musulmi abin da ba su yi ba a baya, hakan ya sa mutane suka zaci kudirin 2019 ya mutu.

Lokaci kadan bayan jam’iyar adawa ta APC ta karbi mulki a 2023 wasu abubuwa na rashin jituwa tsakanin masu mulki da Sarkin musulmi suka rika bayyana, abin da ya kawo mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya daidaita lamarin a baya in da ya sanar da al'umma martabar Sarkin musulmi daga nan ne aka ga gwamnati ta gyara dangantakar ta da Sarkin musulmi a zahiri.

Kwatsam a makwannin  da suka  gabata ne Gwamnati ta fitar da bayanin gyaran fuska ga dokar masarautu wadda aka zargi za a rage karfin ikon Sarkin musulmi abin da ya kai ga wasu na goyon baya wasu ba su goyon baya a tsakanin manyan jam'iyun siyasa biyu APC da PDP a jihar Sakkwato.

A jawabin da kwamishinan shari'a na jiha  ya ce gyaran dokokin masarautu da ke shashi na 76 kashi na 2 da ya shafi nada uwayen kasa da hakimmai an daidai ta shi, tsarin shi ne majalisar sarkin musulmi za ta rika gabatar da bukata ga Gwamna domin nada wadanda ake so uwayen kasa da hakimmai.

Ya ce sabuwar doka na nuni da cewa damar nadawa da majalisar Sarkin muslmi take da ita an mayar da ita gaban gwamna, "shi ne gyaran fuskar da aka yi."

Jam'iyar PDP a Sakkwato ta gargadi gwamnatin jiha kar ta kuskura ta taba Sarkin musulmi, sakataren yada labarai na jam'iyar Hassan Sahabi Sanyinlawal ya ce jam'iyar su na duba yiwuwar zuwa kotu kan sarakunan da gwamnatin jiha ta cire.

"Ina gargadin gwamnatin Sakkwato kar ta kuskura ta yi yunkurin cire Sarkin musulmi nasan yana cikin taken su a lokacin yekuwar zabe, sabon gwamna, sabon sarki, yakamata su jingine wannan tunani.

"Sarkin musulmi ba wai sarkin gargajiya ba ne shugaba ne na musulmin Nijeriya kan haka duk wani yunkuri na cire shi mutanen kasa ba za su aminta ba. 

"Kudirin dokar da aka mika a majalisa za mu kalubalanci haka a matakin shari'a ba za mu kyale duk wani da zai kai ga taba martabar sarakuna ba," a cewarsa.

Alhaji Yusuf Dingyadi ya yi kira ga gwamna kar ya kawo abin da zai haifar da hatsaniya a jiha.

Ya ce masarauta abu ne da ke kare marta da addini abin da ya shafe sama da shekara 100 da kafawa bayan jihadin Shehu Danfodiyo, wuri ne na addini ya kamata a darajanta ta.

Kwamishinan yada labarai na jiha Sambo Bello Danchadi ya ce wasu mutane ne da ke son likawa gwamna kashin kaji suka fito da maganar tsige sarkin musulmi wannan lamari karya ce.

Ya ce dangantaka tsakanin masarauta da gwamnati lafiya lau take ba wata matsala don haka masu rura wutar rikici su koma wani wuri ba su samu shiga anan ba.