Sanata Lamido Ya Faranta Rayuwar Dalibai 1315 Dake Yankinsa A Sakkwato
Sanata Ibrahm Lamido dake wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas a majalisar dattijai ya daukin nauyin biyan rabin kudin makaranta ga dalibban da ke karatu fannoni da dama a jami’ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato.
Sanata Lamido ya sha alwashin taimakawa dalibban in da jami’a ke neman su biya kudi sama da miliyan 80 shi zai biya rabi yayin da gwamnatin jihar Sakkwato ta biyawa dalibban rabi sama da miliyan 43 kenan don tabbatar da karatun su bai samu matsala ba saboda rigimar tattalin arziki da ake fama da shi.
Malam Sani Abdurrahman Bala ne ya wakilci Sanata a wurin soma bayar da tallafin da aka yi a ofishinsa na yanki dake cikin Sakkwato ya ce Sanata Lamido ya daura mana nauyin zakulo dalibban dake yankin Sakkwato ta gabas dake karatu a jami’ar Usman Danfodiyo domin ya tallafa masu ganin halin da ake ciki a kasar nan.
“Mun samu dalibi 1315 ana bukatar su biya kudin makaranta sama da miliyan 80 abin da Sanata ya shigo ciki kenan don ba da gudunmuwa, za mu tantance su a bayar da kudi domin cigaba da karatunsu,” in ji Malam Bala.
Dalibban da suka amfana da gudunmuwar sun godewa Sanata kan taimakawa karatunsu da yay i domin wasu har sun rubuta takardar jingine karatu a wannan shekarar.
Aliyu Sama’ila ‘ni dalibi ne na amfana da wannan tallafi da ban samu wannan taimakon ba zan ajiye karatuna ne domin ban da halin da zan iya biyan kudin makaranta sama da dubu 30 domin mahaifana talakawa ne kuma ni sana’ar da nake yi ba ta da wani karfi gaskiya.’
managarciya