Sau 3 Ina Ƙoƙarin Kashe Mahaifina Domin Na Ci Gado---Ɗan Mai Kuɗi

Sau 3 Ina Ƙoƙarin Kashe Mahaifina Domin Na Ci Gado---Ɗan Mai Kuɗi

'Yan sanda a jihar Kano sun kama wani matashi ɗan shekara 25 Nasir Kabir tare da ƙaramar bindiga da ake kira pistol a unguwar Gadon Ƙaya cikin birnin Kano.
Kabir ya yarda da cewa sau uku yana yunƙurin kashe mahaifinsa domin ya ci gadon kuɗinsa in da zai more tare da abokansa.
Ya ce ya yanke shawarar kashe mahaifinsa a lokacin da ya ga abokansa sun samu gado mai yawa bayan ubansu ya mutu a shekarar 2018 har suka sayo mashin.
Ya maganta da manema labarai a lokacin da 'yan sanda suka gabatar da shi ya ce mahaifinsa ba ruwansa ina sonsa, kuma yana kula da ni, na yi yunƙurin kashe shi don na ci gadon kuɗin da ya tara, na yanke haka don ganin yanda abokai na suka gadi kudi masu yawa.
"a farkon yunƙurin da na yi a shekarar 2018 lokacin ina Makarantar Sikandare na yi amfani da guba waton Maganin Ɓera  amma bai ya tsira. A wannan lokacin na ɗauke motarsa ba tare da ya sani ba na samu haɗari da ita tsawon wata uku ban tafi hida ba. A lokacin na yanke shawarar samun bindiga, wani abokina Saifullahi Sani ya faɗamin in da zan samu bindigar da zan yi amfani da ita, ta sayarwa ce, na karɓo bindigar ina kusa da wurin ina harbin iska anan ne aka kamani ban kai gidanmu ba,." a cewarsa.