Kungiyar Kwadago Ta Shure Maganar  Karin  Farashin Man Fetur

Kungiyar Kwadago Ta Shure Maganar  Karin  Farashin Man Fetur

 

Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fatali da ƙarin kuɗin litar man fetur zuwa N617, inda ta bayyana ƙarin a matsayin abinda ƴan Najeriya ba za su amince da shi ba. Jaridar Daily Trust tace ƙungiyar ƙwadagon a yayin da ta ke martani ta hannun shugaban sashin watsa labarai da hulɗa da jama'a, Kwamared Benson Upah, ya bayyana cewa ƙarin babbar barazana ce ga ƴan Najeriya. 

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙarin barazana ce ga kasuwanci, walwala, hanyar samun kuɗin shiga da rayuwar ƴan Najeriya wacce ta ke ta shan duka ta kowane fanni. 
Ƙungiyar ƙwadagon ta shawarci gwamnatin tarayya da ta dawo daga hanyar da ta ɗauka na shilla farashin man fetur zuwa N1,000 a lita ɗaya, rahoton Leadership ya tabbatar. 
NLC ta yi mamakin ta yadda farashin man fetur ɗin yake tafiya zai taimaki ƴan Najeriya da tattalin arziƙin ƙasar musamman yadda ake ta maganar kawo sauyin da zai amfani mutane.
Sabon farashin man fetur ɗin a cewa ƙungiyar NLC ya nuna cewa nan bada daɗewa ba zai jiyo ƙamshin N1,000 ko fiye da hakan kan lita daya. Ƙungiyar ta ƙara da cewa hakan zai ƙara tsawwala tsadar rayuwar da ake fama da ita. 
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin Tinubu da ta taka burki kan wannan hanyar da ta ɗauko, inda ta ƙara da cewa mutane basu jindaɗi kwata-kwata, sannan kada fa a ɗauki shirun da ta yi a matsayin gazawa ce. 
A wani labarin kuma kun ji cewa ƴan Najeriya da dama sun fara dawowa daga rskiyar gwamnatin Shugaba Tinubu kan ƙarin farashin man fetur. Mutane da dama da aka samu jin ta bakinsu sun yi Allah wadai da wannan sabon tsarin wanda zai ƙara jefa rayuwar talaka cikin ƙunci.