Kungiyar Dalibai Ta Shirya Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Kamun Wanda Ya Soki Aisha Buhari

Kungiyar Dalibai Ta Shirya Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Kamun Wanda Ya Soki Aisha Buhari

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi Allah-wadai da tsare Aminu Adamu bisa wani rubutu da aka yi a Twitter kan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

Shugaban kungiyar, Usman Barambu ne ya fadin hakan a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai wadda Leadership ta samu.
Ya kuma ba da sanarwar wata zanga-zangar da za a yi a fadin kasar a ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 don matsa lamba dan ganin an sako Aminu.
Sanarwar ta kara da cewa, “A ci gaba da yunkurin da muke dashi na ganin nan tabbatar tare da kwatowa kowanne dalibi yanci, muna so mu sanar da shugabannin, masu fada aji, yan siyasa sarakuna da su saka baki dan ganin an sako wannan yaro."
Sanarwa ta kara da cewa: “Ana sanar da ku matakin da shugabannin kungiyar daliban Najeriya da suka dauka na ci gudanar da zanga-zanga a fadin kasar,” 
"Mun yi tuntuba tare da neman an saki dalibin . kuma muna sanar da jama'a zamu fara wannan zanga-zangar a Jami'ar Tarayya Dutse a ranar Litinin 5 ga Disamba, 2022 a fadin kasar."