Ɗan Majalisar Tarayya Ya Gina Katafariyar Police Station A Mazaɓarsa Dake Jihar Kebbi

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Gina Katafariyar Police Station A Mazaɓarsa Dake Jihar Kebbi

Honarabul Kabir Ibrahim Tukura Yana Daf Da Kammala Aikin Ginin Sabuwar Ma'aikatar Yan Sanda Police Station Da Ke Garin Ribah A Jihar Kebbi,

Daga Abbakar Aleeyu Anache

Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Zuru Fakai Danko wasagu da Sakaba da ke jihar Kebbi Honarabul Kabir Ibrahim Tukura yana daya daga cikin membobin da suka shahara a fadin jihar Kebbi wajen aiwatar da ayyukan raya kasa, 

Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya kafa tarihi a jihar Kebbi bayan ya kusa kammala ginin sabuwar katafaren cibiyar yan sanda Police Station a garin Ribah karamar hukumar Danko Wasagu, 

Tukura ya cinma nasara wajen gina katafaren ma'aikatar yan sanda domin tabbatar da tsaron al'umma tare da dukiyoyinsu, a kananan hukumomin Zuru Fakai Danko wasagu da Sakaba,

Ma'aikatar yan sandar itace mafi girma kaf a fadin kananan hukumomin wanda ta samu Kyakkyawan muhalli da tsari cikin babbar Police Station garin Ribah,

Baya ga haka Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya kan samar da ababen cigaba a yankunan mazabunsa da yake wakilta kama daga masana'antu makarantu cibiyoyin al'amuran da suka jibanci cigaban al'umma da dama,

Duba da irin ayyukan raya kasa da jinkan al'ummar mazabunsa da Honarabul Kabir Ibrahim Tukura yake yi ne yasa tuna aka soma fatan ya kara zama wakilin wannan yankin 2023:

Domin a cewar masu irin wannan nazari icen da ya yi kama da shi ake kota kuma juma'ar da za tayi kyau daga laraba ake gane ta kuma mai kamar zuwa ake aika haka kuma tamkar ajiye kwarya ne a gurbinta 2023:

 Abbakar Aleeyu Anache