Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU). Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.
Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.
Dalibin da ya bude shagon siyar da abinci ya ce yajin aikin ASUU ya bashi damar fara sana'a tare da habaka ta cikin kankanin lokaci a birnin Sokoto.
“Na karbi hayar shago, na dauki ma’aikata takwas domin kula da fannin siyar da shayi, indomie, sayar da kayan sha na kwalba da gwangwani, masa, shinkafa da wake, farfesu da nama da ma fannin POS. “Muna siyar da farantin abinci daga N200 zuwa sama daidai bukatan kwastoma."
Ya ce ya kama shagon ne a titin Fodio a tsakiyar birnin na Sokoto, kuma alamu sun nuna kwalliya na biyan kudin sabulu, domin kuwa yana ma da shagon siyar da kayayyakin sanyawa na mata da maza a gefen da dalibai suka fi yawa.
Ya ce yana farin ciki da yadda ya ba matasa aikin yi, kuma ya zuwa yanzu yana da ma'aikata har 10 a shagunan nasa. Ya kuma bayyana cewa, yanzu dai ya fi karfin tambayar iyayensa kudi, domin yana samun kudaden shigan da ke iya magance masa matsalolin kudi.
Abin mamaki, ya ce sam bai karbi bashin banki ko wasu mutane ba, kuma bai nemi wani tallafin matasa daga gwamnati ba. Ya ce, ya fara sana'ar rarraba kaji da kwai tun lokacin da annobar Korona ta bullo, kuma a nan ne ya dan hada kudaden da suka zame masa jarin fara kasuwa. Kasuwa mai bukatar jama'a ce, don haka ya samu damar sanin jama'a da dama da kuma wuraren cin abinci, inda yake kai kaji da kwai, rahoton Daily Nigerian.
A bangare guda, ya shawarci matasa da su kama sana'a kafin dare ya yi musu, domin hakan ne zai iya zame musu silar arziki da za su iya rike kansu.
Hakazalika, ya yi kira ga gwamnatin Buhari da ta duba lamurran malaman jami'a da makomar dalibai domin dinke barakar dake tsakani.
Hakan ke nuna yajin aikin ya samar da nasara sosai tun da dalibban sun fara gane rungumar sana'a shi ne mafi kyautawa ga rayuwa ba rungume boko kawai ba..