Zanga-zanga:DSS ta kama telolin da ake zargin suna ɗinka tutar Rasha a Kano

Zanga-zanga:DSS ta kama telolin da ake zargin suna ɗinka tutar Rasha a Kano

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta kama wasu teloli da ake zargin suna ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano.

DSS ta ce mutanen na da alaƙa da tutocin da aka ɗinka wanda kuma aka rarraba a jihar.

Hukumar ta ce ta kuma kama waɗanda suka ba su aikin ɗinka tutocin, tana kuma ci gaba da bincike.

An dai ga ɗaruruwan masu zanga-zanga yawanci daga arewacin Najeriya rike da tutar Rasha

Ba a san dalilin kawo Rasha cikin zanga-zangar ba, to amma ana fargabar za a iya bai wa lamarin wata fassara ta daban.