Kotu Ta Ƙi Bayar Da Belin Matashin Da Ya Take Ƙafar Ɗaliba A Sakkwato

Kotu Ta Ƙi Bayar Da Belin Matashin Da Ya Take Ƙafar Ɗaliba A Sakkwato

Babban Lauyan Jihar Sokoto (AG), Mista Suleiman Usman, SAN, ya karbi ragamar gurfanar da Aliyu Sanusi-Umar, da ake tuhumarsa da laifin tukin ganganci da kuma haddasa yanke kafar wata ɗaliba.

An gurfanar da Aliyu Umar, mai shekaru 18, dalibi, mazaunin birnin Sokoto, bisa laifin tukin ganganci, tukin mota ba tare da lasisin tuki ba, wanda ya haddasa munanan raunuka tare da yanke kafar ɗan Adam.

An bayyana cewa wanda ake zargin ya tuka mota ne  ya take ƙafar  Fatima Suleiman  jim kadan bayan ta rubuta jarabawar kammala karatunta na shekarar karshe a Sikandaren Khalifa International College Sokoto.

Matar ta samu munanan raunuka inda aka garzaya da ita asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato (UDUTH), inda aka yanke mata kafar.

Hakan ya faru ne saboda karaya da tsananin raunuka da aka yi mata a kafar da ke bukatar kulawar gaggawa.

Usman ya gabatar da bukatar ne a zaman da aka ci gaba a ranar Litinin din da ta gabata inda ya bayar da misali da tanadin kundin tsarin mulki da ya bai wa AG damar daukar nauyin hukunta duk wani laifi da wata hukuma a jihar ta fara.

Kwamishinan shari'a  wanda ya samu wakilcin Mista Sufyanu Maikulki, ya dogara ne da sashe na 211 na kundin tsarin mulkin kasa da kuma na 106 na hukumar shari’a ta jihar Sakkwato wajen goyon bayan bukatarsa.

A hukuncin da ta yanke, Alkalin Kotun, Mariya Haruna Dogon Daji, ta amince da bukatar lauyan gwamnati  ta karbe karar.

Sai dai Haruna DogonDaji, ta ki amincewa da bukatar belin da Lauyan mai kare wanda ake tuhuma  Jocob Ochidi, SAN, ya mika a madadin wanda ake kara.

Bayan gardama kan bukatar gaggauta sauraren karar, musayar bayanai masu kamanceceniya da kwafin karar tsakanin bangarorin, babban alkalin kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar Litinin domin sauraren karar. 

Haruna DogonDaji ta bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a babban gidan gyaran hali da ke Sokoto.

Manema labarai sun  ruwaito cewa zaman kotun ya kasance cikin tsauraran matakan tsaro yayin da ‘yan sanda dauke da makamai ke gadin harabar domin tantance masu kara da jama’a ciki har da ‘yan jarida kafin shiga.

Rashin yiwa Aliyu adalci a wannan shari'ar abu ne mai ban mamaki ganin shi dan asalin jihar Sakkwato ne da ba komai yakamata ya samu adalci a jiharsa ta haihuwa.

Cigaba da tsare Aliyu sama da wata daya  rashin adalci ne da tauye hakkinsa da kundin tsarin kasa ya ba shi, domin laifin da ya aikata wanda ake bayar da beli ne, a jira ganin abin da shari'a za ta wanzar.

Aliyu na buƙatar adalci a wurin mahukunta domin tsare shi a gidan Yari zalunci ne, da babu dalilin haka, domin ba ɗan ta'adda ba ne ko wani da ya saba aikata laifi da ake ganin sakin zai zama barazana ga zaman lafiyar jiha, kan haka yakamata a ba shi haƙƙinsa na shaƙar 'yanci a cigaba da shari'a, har ƙarshe a aiwatar da abin da Allah ya ƙaddara bisa ga doka.