Gwamnan Kano ya bada umarnin bincike kan kwangilar siyan magunguna
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta cewa yana da masaniya kan zargin bada kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Gwamman ya bada umarni ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar da ya gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da gabatar da rahoto domin daukar mataki.
Gwamnan ya kuma bukaci al'ummar jihar da su yi hakuri su jira sakamakon binciken.
managarciya