Kamfanin Janareta Mikano ya ƙaryata yana da  alaƙa da Atiku

Kamfanin Janareta Mikano ya ƙaryata yana da  alaƙa da Atiku

 

Hukumomin kamfanin Mikano International Limited, masu tallata injin bada wutar lantarki na Mikano, sun musanta rahotannin da a ke cewa kamfanin mallakar dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne.

 
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wasu masu amfani da shafin Twitter sun yi ikirarin cewa Atiku babban me hannun jari na kamfanin wutar lantarki da aka kafa a shekarar 1993.
 
Sun kuma yi zargin cewa Atiku ba zai gyara kalubalen da ake fuskanta a fannin wutar lantarkin Najeriya ba idan ya zama shugaban kasa saboda kamfanin mallakar sa ne.
 
Da yake mayar da martani ga ɗaya daga cikin sakonnin twitter, Atiku ya yi watsi da ikirarin, yana mai cewa duk kamfanonin da ya mallaka suna cikin jama’a.
 
“Aboki na wannan ba gaskiya ba ne, amma kun riga kun wallafa a twitter. Ina da manyan kamfanoni kuma an san su a duniya, me ya sa zan musanta wannan? " Atiku ya tambaya.
 
Yayin da yake lissafa dukkanin kamfanonin da yake da hannun jari a cikinsu,  Atiku ya ƙara karyata jita-jitar da ake yaɗawa cewa kamfanonin sun fara aiki ne a lokacin yana mutum na biyu a Najeriya, yana mai jaddada cewa wasu daga cikin kamfanonin sun fara aiki tun shekaru 80.