Sakkwatawa nashan baƙar wuya bisa ƙaracin man fetur a jihar
Matsalar karancin man fetur ta karu a jihar Sakkwato sakamakon rufe gidajen man fetur da aka yi a birnin jiha.
Karancin man fetur ya sanya dogayen layi a gidan Man AA Rano da Matrix domin su kadai ne suka bude suna sayarwa kan 750 zuwa 800.
Mutanen jiha sun shiga bakar wahala in da 'yan bunburutu ko Black market ke cin karensu ba babbaka in da suke sayar da galan daya mai daukar lita hudu zuwa biyar kan kudi naira dubu bakwai ko saye ko bari.
Muhammad Kabiru da ya saye galan daya kan 7000 a titin Kaduna unguwar low-cost a birnin jiha ya shaida ma wakilinmu bakar wahalar da ake sha.
"Samun mai da bakar wuya wannan ma dana saye domin wani da ya Sanni ne ya sa baki aka sayarmin, suma masu sayar da man kan titi sun kwaikwayi masu gidajen mai boye man suke yi don a rika sayar da shi da tsada."
Ya ce gidajen man fetur da ke cikin garin Sakkwato sun fi 100 amma ba 10 dake bude ba don babu man ba sai don Sheri, masu black market sai ka bi layi kake samun man a wurinsu.
Ya yi kira ga gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu da ya zagaya a gidajen man jiha ya kuma dauki mataki ga duk wanda ya samu ya boye mai a gidansa, hakan zai kawo sauki a jihar.
A binciken Managarciya ta gano galan ɗaya ya kai Naira 14000 da wahala ake samun man, a wasu gidajen mai ana sayarwa naira 1000 zuwa sama da haka.
managarciya