'Yan bindiga Sun Kai Hari A Kasuwar Goronyo

'Yan bindiga Sun Kai Hari A Kasuwar Goronyo

'Yan bindida dauke da miyagun makamai sun kai hari a Kasuwar Goronyo a karamar hukumar mulkin Goronyo a jihar Sakkwato da marecen Lahadin nan.

'Yan bindigar sun yi kan mai uwa da wabi in da jikkata mutane da dama har zuwa hada wannan rahoto ba a tantance yawan adadin ba da kuma halin mutanen ke ciki na rasa rayuwa. kamar yadda wata majiya ta shedawa Managarciya.

Maharan sun zo ne a kasuwar suka yi ta harbe-harbe bayan sallar Magrib, ba a san yawan adadin da lamarin ya rutsa da su ba.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ASP Sanusi Abubakar ya ce bai da masaniya kan lamarin amma dai zai bincika ya sanar daga baya.