Gwamnan Katsina ya kaddamar da kwamitin tsara taswirar cigaban Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam, Dikko Umaru Radda, a ranar Talata 22nd Agusta, 2023, ya kaddamar da kwamiti mai mutune 20 da za su taimaka wajen tsara taswira mai inganci da za a yi amfani da ita don kara habaka ci gaban jihar Katsina.
Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Hon. Faruq Lawal Jobe. Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Sakataren gwamnatin jihar Katsina, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, kwamishinan Kudi, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, kwamishinan raya karkara, kwamishinan Ilimin na firamare da na Sakandare, da kuma na kwamishinan ilmi mai zurfi da horar da sana'o'in hannu.
Sauran sun hada da wakilan Masarautar Katsina da Daura, Majalisar Malamai ta Jiha, kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin kwadago da Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha da dai sauransu.
Da yake bayyana nauyin da aka dora wa kwamitin, Gwamna Malam Dikko Radda, ya ce kwamitin na da hurumin sake duba daftarin shirin raya jihar Katsina, bayan nazarin tsare-tsaren ci gaban jihohin Jigawa da Kaduna da kuma Kano da ke makwabtaka, da nufin daukar wasu kyawawan ayyuka da tsare-tsaren da suka dace da hakan zai kara karfafa ingantaccen tsarin ci gaban jiha.
Gwamnan, ya ce kwamitin zai kuma tattara tare da nazari da kuma hada bukatu na al’umma wadanda suka dace da dabarun shirin ci gaban Katsina, tare da hada manufofin da suka dace daga cikin daidaiton rahoton tsarin ci gaban jihar.
Malam Dikko Umaru Radda, wanda ya taya mambobin kwamitin murna, ya yi fatar za su kammala aikinsu, cikin lokacin da aka kayyade musu, su mika rahoton ga gwamnatin jihar Katsina.
managarciya