BADARU YA YI GANAWAR SIRRI DA 'YAN TAKARAR GWAMNA A JIGAWA

BADARU YA YI GANAWAR SIRRI DA 'YAN TAKARAR GWAMNA A JIGAWA
BADARU YA YI GANAWAR SIRRI DA 'YAN TAKARAR GWAMNA A JIGAWA
Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi wata ganawar sirri da daukacin 'yan takarar Gwamna na jam'iyyar  APC a jihar Jigawa. 
Gwamnan ya kira masu neman tsayawa takarar ne domin su samar da ‘yan takara guda daya a tsakaninsu gabanin zaben fidda gwani. 
Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka halarci taron sun hada da mataimakin gwamna, Alhaji Umar Namadi, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, da Sanata Mohammed Sabo Nakudu da dai sauransu.