Biyana Bashin Garatitu Na Lokcin Bafarawa Da Wamakko
Dan takarar dan majalisar dokokin jiha da zai wakilci Sakkwato ta Arewa ta daya Honarabul Muhammad Malami Galadanci da aka sani da Bajare ya yabawa Aminu Waziri Tambuwal kan kalamansa da ya gabatar cewa ya biya bashin garatitu da gwamnatin Attahiru Bafarawa ta bari sai dai bai aminta da cewa gwamnatin Wamakko ta bar bashin da har kuma ya biya.
Tambuwal a jawabinsa ya ce a lokacin da ya shiga ofis a shekarar 2015 ya bayar da umarnin a biya malaman Furamare ariyas na garatitun da suke biya bashi daga bakin shekara 2000 zuwa 2008, bayan nan kuma ya sake biyan bashin wasu shekarru takwas daga 2009 zuwa 2017.
Tambuwal ya ce a wannan biyan za a biya ma'aikatan kananan hukumomi da malaman furamare da suka ajiye aiki daga watan Maris na 2017 zuwa Yau(Okotoba 2022).
Malami Bajare ya ce ba shi da masaniya kan bashin gwamnatin Bafarawa amma yana da ja kan gwamnatin Wamakko ganin yanda Tambuwal ya yi jawabinsa ba wata makama a cikinsa.
Bajare ya ce Tambuwal bai fadi nawa ya kashe a dukkan biyan guda uku da ya yi ikirari ba, bai fadi yawan adadin mutanen da suka ci gajiyar ba, "don haka za mu kalubalanci Tambuwal da hujjojinmu kan gwamnatin Sanata Wamakko data gabata don mutane su san gaskiya da akasinta," a cewar Bajare.
Ya ci gaba da cewa bai kamata Tambuwal ya manta suna da hujjoji rike a hannu kan kudin bail out da ya karbo kusan sau uku da nufin ya biya garatitu na kananan hukumomi da Malaman furamare da ma'aikatan jiha amma ba a yi wani abu ba sai yanzu aka fito da wannan shewar ta 'yan matan amarya.