‘Yan Sanda Sun Kama Barawon Da Ya Saci Mashin 15 a Asibitin UDUTH Sakkwato

‘Yan Sanda Sun Kama Barawon Da Ya Saci Mashin 15 a Asibitin UDUTH Sakkwato

Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta samu nasarar  kama barawon da ya saci Mashin 15 a asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo dake Sakkwato tare da wasu mutum uku da yake sayarwa bayan ya sato.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Gumel ya gabatar da mutanen ga manema labarai ya ce sun samu nasarar kama barawon mai suna Yasir Shehu mazauni  unguwar Bado a birnin jiha.

Ya ce sun kama matashin ne bayan ya saci mashin Yamaha a asibitin UDUTH na wani Mustapha Abddullahi da ya tafi ganin likita.

“a lokacin bincike barawon ya amsa laifinsa na satar mashin din kuma wannan shi ne mashin na 15 da ya sace a lokaci da wurare daban-daban.

“akwai mutum uku da ake zargi da sayen kayan satar Jabiru Abubakar da Kabiru Bashar da Muntaka Ibrahim. Za a cigaba da bincike domin nemo kayan jama’a da suka sace.