Sabuwar alaka ta kullu tsakanin Sanata Lamido da jam’iyar PDP

Sabuwar alaka ta kullu tsakanin Sanata Lamido da jam’iyar PDP

 

Tun bayan da tsamin danganta ta bayyana tsakanin jagoran jam’iyar APC a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido ake ta wasan buya da nemawa kai mafita a tsakaninsu, in da suka shata layi kowanensu ya dauki magoya bayansa, abin da ya kai ana cikin jam'iya daya amma ba a ga maciji adawa ta yi tsanani.

Wasu magoya bayan Sanata Lamido suna ganin abin da yake yi hakan ya dace kuma zai iya samun nasara domin kowa wurin Allah yake nema kuma shi yake bayarwa.

Honarabul Buhari Shaikh Sidi Attahiru yana da yakinin wannan tafiyar ta Sanata Lamido za ta haifar da cigaba a jihar Sakkwato kamar yadda ya soma a wakilcin da yake yi wa Gabascin Sakkwato. 

"Hanyar Sanata tana bullewa kasan akwai bambanci tsakanin mai nema wurin wani da mai nema ga Allah, shi Lamido na kokarin yin abin da ya yiwa al'umma alkawali, saboda hakan Allah zai ba shi nasara, ai an taba samun irin haka a baya a nan Sakkwato lokacin da Sanata Wamakko ya zama gwamna bai tare da Gwamna a lokacin, kuma  dukan  jagorori a lokacin ko daya basa goyon bayansa, amma Allah ya ba shi mulki."

Wasu masu sharhin siyasa a jihar na ganin Sanata Lamido yana son barin jam'iyar APC ne kawai saboda haka ya fara rigima da jagoranta, domin in ba hakan ba ya za a yi uwar jam'iya ta kasa ta ajiye tsagin gwamna wanda yake saman kujera da minista biyu da Sanata daya, ta dauki sanata daya a tafi neman kujerar gwamna hakan ba zai yiwu a lafiyayyen hankali ba.

A ranar Assabar da ta gabata ne Sanata Lamido ya hadu da dan takarar gwamna a zaben da ya gabata na 2023 Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma a wurin daurin aure, bayan an kammala suka hadu a gidan dan majalisar tarayyar da yake wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Alhaji Bello Isah Ambarura in da suka yi liyafa aka tattauna tare da yin hotuna.

A al'adar siyasar jihar Sakkwato mafiyawan 'yan siyasar na jihar, ba su bambanta hulda da siyasa a duk sanda dan siyasa yake hulda da kai tau jam'iyarka yake yi, kan haka ya sanya mutane da dama suka fassara cewa Sanata Lamido ya fara shirin komawa jam'iyar PDP daga APC.

Mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko kan yada labarai Bashar Abubakar ya yi shagube kan shafinsa na Facebook ya ce "'yan aware dai sun fara nuna alkiblarsu! Mu je zuwa...", anan take mataimaki na musamman ga Sanata Lamido Imam Imam shi ma ya yi magana ya ce "Mu fa a wannan kadamin Allah(S.W.T) kawai muke tsoro,"

Wakilinmu ya nemi Sanata Ibrahim Lamido domin samun karin bayani a wannan dangantakar da ta bulla tsakaninsa da mutanen PDP amma dai hakar mu ba cimma ruwa ba, domin ba ya kusa ga waya a lokacin da ake kiransa.