Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
Kungiyar masu harkar saye da sayar da ma'adinan kasa ( Miners Association Of Nigeria) ta sha alwashin hada guiwa da kungiyar Destiny Group dan marawa dan takarar kujerar gwamnan Neja, Hon. Umar Muhammad Bago na jam'iyyar APC. Shugaban kungiyar, Hon. S. D Mambo ne ya bada tabbacin lokacin da ya ziyarci shugaban kungiyar Destiny Group, Hon. Umar Muhammad Saba Bida a sakatariyar kungiyar da ke Minna.
Hon. Mambo, ya cigaba da cewar gwamnatin tarayya ta amince da dokar baiwa matasa damar neman shugabanci dan damawa da su a harkokin shugabanci, wanda jam'iyyar APC ta samu nasarar tsayar da dan takara matashi wanda yake da kwarewa dan ya wakilci karamar hukumar Chanchaga a majalisar wakilai ta kasa har karo uku, dan haka muna da tabbacin idan ya zama gwamnan Neja zai yi anfani da kwarewarsa ta shugabanci wajen kawo cigaba a jihar nan.
A cewarsa muna bukatar kwararren gwamna da zai dubi bangaren masu harkar ma'adinan kasa wajen samar masu da kayan aiki na zamani, da kuma kokarin ganin an sakarwa masu hakar ma'adinai mara musamman ganin kungiyar na kokarin tsaftace yayanta musamman duba da halin matsalar tsaron da jihar nan ke fuskanta.
Da yake jawabi, shugaban kungiyar Destiny Group ta jiha, yace kungiyarsu an kafa ta ne dan wayar da kan al'ummar jihar Neja muhimmancin marawa jam'iyyar APC a manyan zabuka masu zuwa, duba da irin cigaban da gwamnatin APC ta samar a kasar nan cikin shekaru bakwai zuwa takwas da take akan mulki.
Hon. Saba Bida, yace Hon. Umar Bago gogaggen dan siyasa ne da muke kyautata zaton duk wata matsalar da ake fuskanta a jihar yasan da ita kuma yana da kwarewa wajen magance su.
Destiny Group, tana jawo hankalin al'ummar jihar nan da su yi siyasa mai tsafta dan samun nasarar zabe cikin nasara, wanda shi zai samar da shugabanci mai alfanu a jihar ta Neja.
Darakta Janar, na Destiny Group, Kwamared Bala Kutigi, ya jawo hankalin matasa yan uwansa da su guji siyasar banga da dabanci, domin ba zai haifar da da mai ido ba a manyan zabuka masu zuwa.
Bala Kutigi, yace rangadin sulhu tsakanin yayan jam'iyyar APC da dan takarar gwamnan ya kammala makon da ya gabata abu ne mai alfanu kuma ya haifar da da mai ido, domin an samu gagarumin nasara wajen sulhunta yayan jam'iyyar, wadanda suka yi takara suka fadi a zaben fidda gwani, da ma wasu manyan da ba su farin ciki da yadda zaben fidda gwani ya kasance ba, saboda duk wanda aka yiwa ba daidai ba kamar yadda aka bashi hakuri, to ya dubi girman Allah ya hakura domin jam'iyya ta samu cigaba da samun nasarar babban zabe cikin sauki.
Da yake bayani a wani ziyarar gani da ido da ya kawo a sakatariyar Destiny Group, dan takarar gwamnan jihar Neja a jam'iyyar APC, Hon. Umar Muhammad Bago, ya yabawa kungiyar musamman wajen hada kungiyoyi waje daya dan yin tafiya tare.
Yace muna da kudurce-kudurce masu alfanu a jihar nan idan Allah ya ba mu nasarar cin zabe, wanda wannan nasarar bai samuwa dole sai mun ajiye bambance bambancen da ke tsakanin mu dan yin tafiya tare, ina da tabbacin da goyon bayan ku, da amincewar ku idan muka dunkulawa jam'iyyar APC za mu samar da cigaban da zamu yi farin ciki a jihar nan.
Taron dai ya samu halartar mata da matasa da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, tare da yin alkawalin goyawa jam'iyyar APC baya dan ganin ta samu nasarar zaben 2023.