NNPC Ya Fadi Dalilin Karancin Man Fetur Da Ake Fama Da Shi

NNPC Ya Fadi Dalilin Karancin Man Fetur Da Ake Fama Da Shi
NNPC Ta Sanar Da Dalilin Karancin Man Fetur a Nijeriya

Kamfani  NNPCL ya bayyana cewa karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon cikas a ayyukan wasu jiragen mai guda biyu.

A cewar NNPCL, matsalar da jiragen ruwan masu dauke da fetur din suka samu ya haifar da tangarda wajen samar da mai da kuma rarraba shi.
Olufemi Soneye, babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a shafin NNPCL na X.
“NNPC na son bayyana cewa tangardar samar da man fetur da rarraba shi da aka samu a wasu sassa na Legas da kuma Abuja ya faru ne sanadin cikas da aka samu a ayyukan wasu jiragen ruwa guda biyu.
"Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana aiki ba dare ba rana tare da masu ruwa da tsaki domin magance lamarin tare da dawo da rarraba man kamar yadda aka saba."