Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Hukuncin Da Take Son A Yankewa Makashin Hanifah

Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Hukuncin Da Take Son A Yankewa Makashin Hanifah

 

Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nuna goyon bayanta kam kalaman malamin addini Shaikh Usman Gadon Kaya  na akai  makashin Hanifa lahira.

 Aisha  ta jawo hankalin sufeta janar na 'yan sandan Nijeriya a lamarin. 

A kalamanta, ta ce  "Muna goyon bayan hukuncin Malam." 
 A ranar 2 ga watan Disamba, 2021, shugaban makarantar yara dake Kwanar Dakata, ƙaramar hukumar Nasarawa, cikin kwaryar birnin Kano, Abdulmalik Tanko, ya sace Hanifa Abubakar
Jami'an tsaro sun samu nasarar kame Tanko, wanda ya karbi dubu 100 a wani sashi na miliyan N6m da ya nema kudin fansa daga mahaifan  yarinyar. 
Shugaban makarantar ya kashe ƙaramar yarinyar mai shekara biyar da maganin ɓera na N100 kacal, kamar yadda ya tabbatar wa hukumar yan sandan Kano.
"Dan haka kamata ya yi a kashe shi, kamar yadda ya halaka ƙaramar yarinya. Kuma idan za'a kashe shi, kamata ya yi a fito fili kowa ya gani, domin gobe kar wani ya maimaita." a cewar Malam Gadon Kaya.