Boot Party Ta Yi Ta'aziya Ga Tambuwal Kan Rasuwar Yayansa

Boot Party Ta Yi Ta'aziya Ga Tambuwal Kan Rasuwar Yayansa


Jam'iyar adawa a jihar Sakkwato Boot Party ta yi ta'aziya ga gwamman  jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kan rasuwar yayansa Muhammadu Bello Wazirin Tambuwal.

Shugaban jam'iyar a Sakkwato Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo ne ya mika sakon ta'aziyar amaadin shugabani da magoya bayan jam'iyar a wata takarda da ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a birnin jiha.

Mai Kassu ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ba ga iyalai da 'yan uwa kadai ba har da  jihar Sakkwato gaba daya tala'akari da irin gudunmwar da margayin ya bayar a wurin taimakon addini da al'ummar kasar Tambuwal.
Shugaban ya roki Allah ya gafarta masa ya baiwa gwamna da al'ummar Sakkwato hankurin rashinsa.
A daren jiya ne Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwa rasuwar dan uwansa wanda yake babba a gidansu waton Alhaji Muhammad Bello Wazirin Tambuwal.
Gwamnan ya ce Wazirin Tambuwal wanda ya kwashe shekara 37 saman karaga bayan ya gadi mahaifinmu Alhaji Umar Waziri Usmanu, ya bar duniya ne da marecen Talata za a yi masa janaza da safen ranar Laraba kamar yadda addini ya tanadar.