Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da sanarwar kashe ‘yan bindiga 50 a Saulawa Farin Ruwa kan hanyar fita karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Kwamishina tsaro Samuel Aruwan ya fadi hakan a jiya ya ce sojoji a jirgi mai saukar Ungulu ya tantance maharan saman babura nan ne ya yi masu kwantan bauna in da aka samu nasarar jikkata sama da maharan su 50.





