Majalisar Dattawa Ta Sake Yin Gyara A Kundin Dokar Zabe, Ta Fayyce Hanyoyin Zaben Fidda Gwani Na Jam'iyu 

Majalisar Dattawa Ta Sake Yin Gyara A Kundin Dokar Zabe, Ta Fayyce Hanyoyin Zaben Fidda Gwani Na Jam'iyu 
Daga Babangida Bisallah, Abuja.
Majalisar dattawa ta sake yin gyara ga kudurin dokar zabe ta 2022 a inda ta fayyace hanyoyin da jam'iyu zasu bi wajen zaben yan takara. 
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abubakar ya gabatar da bukatar sake yin gyara akan kudurin dokar a zaman majalisar na ranar Talata.
A jawabin sa bayan amincewa da gyaran, shugaban majalisar, Ahmad Lawan yace an yi gyaran ne don a daidaita matsayar majalisar dattawan da ta wakilai akan kudurin dokar zaben. 
Lawan yace sake gyaran ya fayyace karara hanyoyin yin zaben fidda gwani na Jam'iyu. 
Yace yana da kwarin gwiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sa ma kudurin dokar hannu don ta zama doka.
Lawan ya gargadi jam'iyun siyasa cewa idan suka ki bin tanaje tanajen dokar akan hanyoyin zaben fidda gwanin zasu rasa damar shiga cikin harkar zaben gama gari. 
Kudurin dokar, a sashi na 84 (2) ya samar da hanyoyin zaben kai tsaye na yan Jam'iya ko ta hanyar wakilai (deliget) ko ta sassanci wajen zaben yan takarar jama'iyun siyasa. 
Majalisar ta yi bayani a sashi na 84 (9) akan zaben yan takara ta hanyar sasanci, inda ta tanaji cewa dole ne dukkan yan takara da aka tantance don takarar su amince a rubuce da janyewar su ma mutum daya, tare da nuna cewa sun janye ne don kashin kan su kuma sun amince da takarar wanda suka janye mawa. 
A yayin da wasu daga cikin yan takarar suka ki bayarda amincewar su a rubuce don samu  dan takara ta hanyar sasanci, kudirin dokar ya umurci jama'iyun da suyi amfani da hanyar zabe na kai tsaye ko na wakilai wajen fitar da dan takara.