APC Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Yi Babban Taron Zabar Shugabanni Na Kasa
APC Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Yi Babban Taron Zabar Shugabanni Na Kasa
Shugaban kwamitin riko da tsare-tsare na musamman na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a ranar 26 ga watan Fabrairu.
Mai Mala ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron mata na Progressive Women Congress da ake gudanar a Babban Birnin Tarayya.
An yi dakon sanin ranar wannan taron tun bayan babban taron gwamnonin APC in da suka sanar da wata ba tare fadin takamaimiyar rana ba.
Bayan zuwan shugaban rikon APC a fadar shugaban kasa aka sake jiran jin ranar, haka ba a fadi ba sai yanzu da Buni ya bayyana wa mutanen kasa.
Bayan sanar da ranar za a jira a fitar da yadda tsarin shugabancin zai kasance waton karba-karba domin sanin in da za a raba shugabannin yanki-yanki kamar yadda Nijeriya ke tafiya Kudu da Arewa.
managarciya