Makarantun Gwamnati A Jihar Jigawa Nafuskantar Ƙarancin Malamai

Jihar ta Jigawa na daga cikin jahohin da suka gaza cika irin wadannan ka'idoji ko sharudda da suka danganci wadatattun ajujuwa da malamai da kuma kayan aikin koyo da koyarwa da suka  dace da suka kuma kamata a ce an tanade su a makaranta don  inganta harkar karatu da koyarwa.  Akwai  makaranta a kauyen Sabolari da ginin ajujuwanta biyu ne kawai kuma akwai dalibai sama da dubu daya dake daukar karatu a makarantar, sannan babu mai gadi babu katanga kuma makarantar daga shugaban makarantar sai malami daya su ne suke koyarwa kuma su ne jagororin tafiyar da makarantar. A wata kididdigar ma'aikatar ilmi ta jihar Jigawa yara sama da dubu dari bakwai 700,000 ne basa zuwa makaranta.

Makarantun Gwamnati A Jihar Jigawa Nafuskantar Ƙarancin Malamai

 

Jihar Jigawa na daya daga cikin jahohin Arewa da ke da tsarin bayar da ilimi kyauta, kamar yadda lamarin yake a dokar ilimi ta jihar, laifi ne babba ga iyayen da suka gaza sanya 'ya'yansu a makaranta.

 

Ilimi babban lamari ne da idan har ba a cika sharuddan  gudanar da shi ba, to kuwa ba zai yiwu ba, domin ko an yi ba zai samu inganci ba.

 
Jihar ta Jigawa na daga cikin jahohin da suka gaza cika irin wadannan ka'idoji ko sharudda da suka danganci wadatattun ajujuwa da malamai da kuma kayan aikin koyo da koyarwa da suka  dace da suka kuma kamata a ce an tanade su a makaranta don  inganta harkar karatu da koyarwa.
 
 Akwai  makaranta a kauyen Sabolari da ginin ajujuwanta biyu ne kawai kuma akwai dalibai sama da dubu daya dake daukar karatu a makarantar, sannan babu mai gadi babu katanga kuma makarantar daga shugaban makarantar sai malami daya su ne suke koyarwa kuma su ne jagororin tafiyar da makarantar.
 
A wata kididdigar ma'aikatar ilmi ta jihar Jigawa yara sama da dubu dari bakwai 700,000 ne basa zuwa makaranta.
 
Wasu dalibai da manema labarai suka  zanta da su, sun bayyana yadda suke daukar darussa a cikin ajujuwan makaranta a takure, in da suke neman dauki don samun walwala.
 
A cewar shugaban wata makaranta  a garin Dutse ya ce suna kai koke wajen gwamnati kan halin da makarantunsu suke ciki amma bayan sun gabatar da  koken  gwamnati ba ta kawo musu malamai ba, su ne suke nemo malaman da za su rinka zuwa suna tallafa musu. 
 
Kwamishinan ilmi na jihar Jigawa Lawal Yunusa Danzomo manema labarai sun yi ƙoƙarin ganinsa domin sanin hoɓɓasar gwamnati a wurin magance matsalolin harkar ilmi a jihar amma lamarin ya ci tura domin baya ofis kuma wayar shi ba ta shiga.
 
 
Daga Hadiza Ado Jinta