Ɗalibar Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Da Ke Katsina Ta Lashe Gasar Hikayata

Ɗalibar Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Da Ke Katsina Ta Lashe Gasar Hikayata

Ɗalibar Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Da Ke Katsina Ta Lashe Gasar Hikayata Ta Gidan Radiyon BBC Hausa Ta Shekarar 2021

Aishatu Musa Dalil ita ce gwarzuwar gasar Hikayata ta bana inda labarinta mai suna 'Haƙƙina' ya yi nasarar zuwa na daya a gasar.

Labarin Haƙƙina labari ne kan wata matashiya mai suna Fatima wadda mijin mahaifiyarta ya yi mata dukan kawo 'wuka' tare da fyaɗe har ya ji mata raunuka masu muni.

Sai dai maimakon mahaifiyarta ta ɗauki matakin nema wa ƴarta magani da kuma kai ƙarar mijin nata, ta rufe Fatima a ɗaki don gudun kada mutane su ji abin da ya faru sannan ta gargaɗe ta kan sanar da kowa batun fyaɗen.

A cewar mahaifiyar Fatima, bayyana abin da ya faru ne saboda "rufin asirina da ke. Idan na faɗa da ni da ke tamkar mun kashe kanmu ne. Wa zai aure ki wa zai aure ni?'

Labari ne da ya bankaɗo wasu manyan matsaloli da ake fama da su a arewacin Najeriya - wato batun ɓoye laifin fyaɗe saboda tsoron ƙyama da tsangwam.

Wace Ce Aishatu Musa Dalil?

Aishatu bafulatana ce ƴar asalin jihar Adamawa amma an haife ta kuma ta girma a garin Kaduna.

Marubuciyar mai shekaru 18 tana shekararta ta farko a sashen koyon Ingilishi da Faransanci a Jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua a jihar Katsina.

An fi saninta da suna Ayshkhair a tsakanin marubutan Hausa.

Ta fara rubutu ne a shekarar 2018 kuma tana matuƙar sha'awar karanta labaran sarauta, a cewarta.

"Tun ina yarinya ina da baiwar ƙirkirar labari in rubuta ko in bai wa mutane. Hakan ya sa na ginu da son rubuta labari.

"Kalubalen da ƴan uwana mata ke fuskanta a wannan ƙarni da muke ciki, yana cikin manyan dalilan da ya sa naƙara ƙarfafa rubutuna," in ji Aishatu.