Yadda Gwamnan Sakkwato da takwarorinsa 12 suka ci bashin kusan naira biliyan 250 a wata shida
Hukumar kula da bashi ta Najeriya ta ce a cikin wata shida sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da Zamfara, da Katsina sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar.
Gwamnonin jihohin na daga cikin gwamnoni 16 na ƙasar da suka ci bashin bayan rantsar da su a kan mulki a cikin watan Mayun 2023, inda hukumar kula da basukan ƙasar ta ce ta haɗa al’ƙaluman ne bayan jumlar lissafin da suka yi kan farashin dala a kan naira 889.
Hakan dai na ƙunshe a cikin wani rohoto da ta wallafa a shafinta na internet, inda ta ce an ci bashin ne a tsakanin 30 ga watan Yunin da 30 ga watan Disamba na 2023.
Rohoton da hukumar kula da basukan ta Najeriya ta wallafa ya nuna cewar gwamnoni 16 na ƙasar sun ƙara yawan bashin cikin gida da ake bin jihohinsu da naira biliyan 509, yayin da na ƙetare ya kai naira biliyan 243 da miliyan 95, da kusan dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 265 da miliyan 37.
Jihohin da suka ci wannan bashi sun haɗa da Katsina, da Zamfara, da Filato, da Naija, da Benue, da Cross River da babban binrin ƙasar Abuja.
Kuma ana binsu bashin cikin gida na naira billiyan 115,57. Yayin da jihohin Kano, da Kaduna, da Niger, da Filato, da Sokoto, da Taraba, da Zamfara, sai Ebonyi da suka ci bashi daga wajen ƙasar da ya kai dala miliyan 125, dai dai da naira biliyan 111, da miliyan 24.
Hukumar dai ta ce basukan da aka ci a cikin gida su ne aka karbo daga masu bayar da bashi da ke Najeriya, yayin da na ƙetare kuma su ne, wadanda aka ci daga bankin duniya, da na bayar da lamuni na duniya.
Hukumar ta Najeriya ta ce cikin gwamnonin da suka ciyo bashi daga wajen bankin duniya ko na bayar da lamuni na IMF sun haɗa da gwamnan Kano da ya karɓo bashin dala miliyan 6.6, sai na Neja da ya ƙarbo bashin dala miliyan 1.27, sannan Filato da shi ma ya karbi bashin dala dubu ɗari 831, sai gwamnan Sokoto da ya ci bashin dubu ɗari 499 da 472, sai na Taraba, da ya ci dala miliyan 1.51 sai na Zamfara da shi ma ya ci na dala dubu ɗari 655 da 563.
Sai gwamnan jihar Kaduna Mallam Uba Sani da shi kuma ya ci bashin dala miliyan 17.69.
Haka kuma ta ce a cikin gida bashin da ake bin jihar Katsina na naira biliyan 36.93 ya ƙaru zuwa naira biliyan 62.37 zuwa naira 99.3 zuwa ƙarshen Disambar shekarar 2023.
Sai jihar Neja wadda ita ma ake binta bashin naira biliyan 17.85 da ya karu zuwa naira miliyan 121. 95 a watan Yuni 2023, sannan ya ƙaru zuwa naira biliyan 139.8 a watan Disambar 2023.
Sauran wadanda suka ci bashi a cikin gida sun hada da jihar Filato da ke da bashin naira biliyan 16.32, sai Rivers da ita ma ta karɓi bashin na naria biliyan 6.75, sannan Rivers mai naira biliyan 7.07, sai Zamfara mai naira biliyan 14.2 sai birnin tarayya Abuja karkashin Ministanta Nyesom Wike da ya ci bashin naira biliyan 6.75
managarciya