Kano ta fi kowacce jiha yawan karɓar katin zaɓe ---Hukumar Zaɓe

Kano ta fi kowacce jiha yawan karɓar katin zaɓe ---Hukumar Zaɓe

 

Jihar Kano ce a kan gaba wajen yawan karɓar katin zaɓe a faɗin ƙasar nan, in ji Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.

Jami’in hulɗa da jama’a na INEC, reshen Jihar Kano Adam Ahmad Maulud ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Laraba a Kano.

Ya ce ofishin INEC na kano ya buɗe sabuwar cibiyar rajista a filin wasa na Sani Abacha, inda ya ce akwaina’urorin yin rijistar sama da guda 30 a wajen.

Maulud ya bayyana cewa sabuwar cibiyar tana aiki sau uku a mako, wato ranekun Talata, Laraba, da Alhamis.

 “A wata sanarwa da ta gabata, jihar Kano ce ta zo ta biyu wajen yin rijistar, amma na yi imani da wannan fitowar da mutane sukai wajen karbar katin zaben, muna kan gaban dukkan jihohin kasar nan.”

Jami’in hulda da jama’ar ya kara da cewa, ɗimbin jama’ar da suka fito domin sake tantance yin katin zabe ya biyo bayan gagarumin gangamin wayar da kan jama’a ne da INEC ta yi kan mahimmancin rajistar.

Idan dai za a iya tunawa INEC ta sanya ranar 30 ga watan Yuli a matsayin wa’adin ranar rufe aikin rajistar.