Nadin sarakunan gargajiya: Aikin addinin musulunci ne muka yi----Sarkin musulmi
Aikin Addinin Musulunci ne muka yi a cewar Sarkin Musulmi
Mai martaba Sarkin Musulmi a lahadin data gabata ya nada sabbin sarautu guda 20 ga wasu manyan mutane a Sakkwato da wajenta bayan kwana 22 da nada mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Maniru Muhammad Dan'iya matsayin Walin Sakkwato.
Sarkin musulmi a jawabinsa ya ce sarautun da aka bayar an yi ne saman cancanta ba tare da shigar da siyasa ba saboda a kara inganta lamurran addini da samun cigaba.
Ya ce bai taba bukin nadi na mutane masu yawa kamar wannan ba an yi hakan ne domin kara bunkasa masarauta da harkokin addinin musulunci a Nijeriya musamman taimakawa masu karamin karfi.
Sa'ad ya ce sun karrama 'yan uwansu na jinin danfodiyo dakuma abokansu da suka taso tare tun yarinta abu guda ne a daular Usmaniya, wadanda suka zo murna su hada da addu'a ga nauyin da ya karu saman kan wadanda aka baiwa sarautun.
"Wadan nan da muka karrama kowanensu ya cancanta ba wanda ya zo ya yi karamar murya don a nada shi, akwai daga cikinsu da suka nemi sarautar shekara 10 da suka wuce sai yau Allah ya kaddari mu yi wannan aikin na addinin musulunci." a cewar Sarkin musulmi.
Ya ce aiyukkan da suke yi na al'umma ne ba su sanya son rai a ciki, dafatar wadanda aka nada ba za su ba da kunya ba kuma nan gaba kadan za su kara jawo wasu musamman a wajen Sakkwato su karramasu domin karin dankon zumunci.
Ya yi kira ga wadanda aka nada su taimakawa mutane su yi azumi cikin sauki.
Sarkin Musulmi ya nada tsohon gwamnan Kogi Ibrahim Idris matsayin Jekadan Sakkwato da tsohon minstan Sufuri Alhaji Yusuf Suleiman Dan Amar na Sakkwato da Ahmad Tijjani Mora Kayayen Sakkwato da Faruk Ahmad Maishanu Danmadamin Sakkwato da Aminu Buhari Galadima Dan malikin Sakkwato da 'ya'ya tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki su uku da sauransu.
managarciya